KWAMITIN zaɓe na Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewacin Nijeriya (‘Northern Nigeria Writers’ Summit’, NNWS) ya zaɓi Dakta Bashir Abu Sabe a matsayin sabon shugaban ƙungiyar.
A ranar Litinin, 16 ga Nuwamba, 2020 ne kwamitin na mutum uku a ƙarƙashin jagorancin Mista Odoh Diego Okenyodo bayyana Abu Sabe a matsayin wanda ya yi nasarar lashen zaɓen da sauran muƙaman da aka yi takara a kan su.
Dakta Abu Sabe babban malami ne a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’Adua da ke Katsina.
Ya yi digirin sa na farko da na biyu a Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo da ke Sokoto, ya samu digiri na uku a Jami’ar Alƙhahira da ke Masar.
Abu Sabe masani ne kan nazarin adabin Hausa a fannoni da dama. Ya yi rubuce-rubucen sa kan abin da ya shafi “adabin kasuwar Kano” da kuma kamanci da bambancin da ke akwai tsakanin marubuta mata a Masar da Nijeriya.
Shi ne shugaban Ƙungiyar Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen Jihar Katsina.
Ya taɓa zama ɗan kwamiti na taron NNWS a 2017 da aka yi a Katsina.
Abu Sabe ya na da kishi da son rubutu da marubuta da adabi gaba ɗaya, inda ya bayar da gudunmawar sa sosai wajen cigaban rubuce-rubuce ta fuskoki daban-daban.
An kafa NNWS ne a garin Minna da ke Jihar Neja a cikin 2008. Ta kasance inuwar marubutan Nijeriya na jihohi 19 da ke Arewa, da nufin tsare-tsaren cigaban marubutan yankin.
A cikin 2018 a Maiduguri, Jihar Borno, aka zaɓi shugabannin riƙo na ƙungiyar a ƙarƙashin shugaban ta, Malam Baba M. Dzukogi, waɗanda su ka tafiyar da ƙungiyar.
Shugabannin da aka zaɓa a jiya su ne:
Dakta Bashir Abu Sabe – Chairman
Omale Allen Abduljabbar – Vice Chairman
Safiya Isma’il Yero – Secretary
Isma’il Bala Garba – Asstistant Secretary
Hussaini Kado – Treasurer
Awaal Gata – PRO (North Central)
Haruna Adamu HAdejia – PRO (Northwest)
Yusuf Garba Yusuf – PRO (Northeast)
Maryam Gatawa – Auditor
Ogbe Benson Aduojo Esq – Legal Adviser
Tee Jay Dan – Ex-Officio 1