HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta bayyana cewa ba ta kama jarumar Kannywood Maryam Yahaya da wani laifi ba game da wani faifan bidiyo da aka yaɗa a soshiyal midiya na wani saurayi da wata budurwa da ta ke yi wa saurayin goge.
Sai dai wannan bidiyo na nuna cewa kamar a wurin bikin auren su ne su ka yi, domin ita budurwar shigar amare ta yi.
An ɗauki bidiyon tare da manna hotunan Maryam Yahaya a cikin bidiyo a nana cewa jarumar ce ta ke yi wa wani saurayi gogen.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce, “Biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da mu ka karɓa a kan wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta na zamani, wanda ke nuna wata matashiya da ake zargin jarumar finafinan Hausa ce ta Kannywood, wato Maryam Yahaya, da yin bidiyon da ya ci karo da dokokin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano.
“A saboda haka, mun gudanar da bincike na musamman tare da samun rashin sahihanci na wannan bidiyo da aka tura mana ƙorafi a kai.”
Ya ci gaba da cewa, “Haka kuma, binciken ya tabbatar da fuskar wacce ta yi bidiyon ba jaruma Maryam Yahaya ba ce, tare da gano cewa wasu gurɓatattun mutane ne ke son amfani da wannan damar domin ɓata wa jarumar suna ta yadda su ka yi amfani da sunan jarumar tare da saka hotunan ta a kusa da bidiyon domin su ja hankalin masu kallo tare da kawo shakku da ruɗani a cikin al’umma.”
Ya kuma ƙara da cewa, “Mu na yin kira tare da gargaɗi ga masu irin wannan halayya ta ɓata wa al’umma suna, musamman ‘yan masana’antar Kannywood, da su kuka da kan su, domin duk wanda hukumar ta samu da irin wannan laifi, to babu shakka zai fuskanci fushin hukuma.
“Haka kuma mu na ƙara jaddada aniyar mu ta ƙara saka ido tare da hukunta duk wanda aka samu da laifin karya dokokin ba tare da sani ko sabo ba.”