Fadila za ta auri wani wanda aka faɗa wa mujallar Fim cewa ya na daga cikin manyan hadiman Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina ne a fagen siyasa mai suna Hon. Tanimu Sada Sa’ad.
A katin gayyatar zuwa ɗaurin auren da aka raba, an nuna cewa za a ɗaura auren fitacciyar marubuciyar ne a garin su, wato Kurfi, Jihar Katsina, a ranar Juma’a, 27 ga wata.
Wakilin mu ya samu labarin cewa ɗaya daga cikin abubuwan ban-sha’awa da ake shiryawa a bikin shi ne gasar rubuta gajerun labarai da waƙoƙi waɗanda za a gabatar a lokacin taron bikin.
Za a yi taron a Katsina a ranar Alhamis.
A ranar Juma’a kuma ɗaurin aure, wanda da zaran an gama shi, shi kenan an sallami kowa.
Tun daga lokacin da labarin auren ya ɓulla, kamar wata ɗaya da ya gabata, marubuta daga wasu jihohin su ke ta shirin tafiya Katsina inda za su haɗu da marubutan da ke jihar, a ci bikin tare da su.
Mujallar Fim ta ji yadda marubuta daga Kano da Kaduna da wasu garuruwan su ke ta bayyana ƙudirin su na halartar wannan biki.
Shugabar ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin marubuta da ake da su, wato Ƙungiyar Marubuta ta Alƙalam da ke Kaduna, Hajiya Halima K/Mashi, ta faɗa wa wakilin mu cewa, “Abin da ya sa ka ga mu na ta ɗokin zuwa bikin Fadila shi ne saboda ita Fadila ba ta yin sanyi-sanyi da duk wata hidima ta marubuta.
“In dai an saka ta a wani sha’ani na marubuta, to sai inda ƙarfin ta ya ƙare; shi ya sa mu ma za mu je domin taya ta murna.”
Ta yi nuni da yadda Fadila ta jajirce wajen tabbatar da nasarar Taron Duniya na marubutan Hausa da aka yi har karo biyu, ɗaya a Kano ɗayan a Kaduna, ta ce lallai Fadila ta cancanci a taya murna da kuma addu’a.
Wata majiya ta shaida wa mujallar Fim cewa tuni kwamitin tsare-tsaren bikin ya shirya wa manyan baƙi abinci da wurin kwana.
Wata majiyar kuma ta kurkusa da Fadilar ta faɗa wa mujallar Fim cewa amaryar za ta tare ne a Kano inda mijin ya ke da gida.
Majiyar ta ƙara da cewa Fadila za ta kasance matar Tanimu ta biyu, domin ya na da uwargidan sa a cikin Katsina.
Wannan shi ne aure na biyu da marubuciyar za ta yi. Auren ta na fari ya mutu ne a ‘yan shekarun baya bayan sun samu ‘ya guda ɗaya mai suna Ibtihal.
To Allah ya sa alheri, ya ba su zaman lafiya, amin.