CI-GABA da shagalin bikin jarumin Kannywood Yusuf Saseen (Lukman a cikin shirin ‘Labari Na’) da amaryar sa Amina Zakari Yunusa Daya ya ci gaba da ƙayatar da jama’a inda har ta kai mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya ba amarya kyautar zunzurutun kuɗi har N400,000, shi kuma ango na jiran tasa babbar kyautar.
Tun a Potiskum, Jihar Yobe, aka ci gaba da rugunɗumin bikin bayan an ɗaura auren Yusuf da Amina, inda aka gudanar da wasan ƙwallon ƙafa a daren ranar Asabar ɗin da aka ɗaura auren, wato 24 ga Disamba, 2022.
An buga wasan a tsakanin ‘yan wasan amarya da na ango a filin wasa na zamani da ke cikin gidan Kori a Socol Junction a Titin Maiduguri a Potiskum.
Wasan, wanda shi ma ango ya buga ƙwallon, an fara shi ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, aka tashi da ci biyu daga kowane ɓangare da misalin ƙarfe 9:00 na dare.
Yusuf Saseen, wanda cikakken sunan sa Yusuf Muhammad Abdullahi, tare da tawagar abokan sa, sun ɗauko amarya da rakiyar ‘yan’uwan ta, zuwa Kano a ranar Lahadi.

Bayan an kawo amaryar, a daren ranar, an tsara shirya gagarumar dina a ɗakin taro na Meenah Events Centre da ke kusa da Gidan Gwamnatin Kano. Har an fara da misalin ƙarfe 8:00 na dare, amma sai aka samu matsalar da ta tilasta dole aka samu sauyin wurin taron zuwa Amani Events Centre da ke Audu Baƙo Way kusa da Prince Hotel, wanda hakan ya sa mutane da dama da ba su san da sauyin ba, ba su samu halarta a kan lokaci ba.
Kuma wannan ya sa ba a fara taron a sabon wurin ba da wuri, sai bayan ƙarfe 9:00 na dare.
Duk da yake mawaƙi Ado Gwanja ya zo a makare, zuwan nasa ya ƙara wa taron armashi inda ya hau kan dandali ya rera waƙoƙin ‘Chas’ da ‘War’ wadda mata da maza su ka yi masa caa har zuwa lokacin da ya kammala, aka fitar da shi daga wajen da ƙyar saboda cincirindon da masoya su ka yi masa.
Haka shi ma mawaƙin siyasa Dauda Adamu Abdullahi Kahutu (Rarara) ya halarci wurin shagalin duk da yake shi ma a makare ya zo, amma kamar yadda ya ce lokacin da ya fito gabatar da jawabi a gaban ango da amaryar, “Duk da na zo a makare, amma ni ne a farko.” Daga nan ya yi wa ma’auratan gagarumar kyauta ta musamman, abin da ya kira da “saƙo zuwa ga ango da amarya”. To amma ya ƙi bayyana ko wace irin kyauta ce, amma dai ya umarci sakatariyar sa wadda su ka zo tare, wato jaruma A’isha Ahmad Idris (A’ishatulhumaira), da ta isar da saƙon zuwa gare su.
Haka kuma a nan take Rarara ɗin ya ba MC da ke wajen kyautar N50,000 ta hannun A’ishatulhumaira, bayan da su ka roƙe shi kyautar mota ko mashin.
Duk da ƙoƙarin da wakilin mujallar Fim ya yi na jin ko menene kyautar da mawaƙi ya yi wa amarya da angon ta bakin sakatariyar sa, ba ta bayyana masa ko menene, domin kamar yadda ta ce ita ma ba ta san ko menene ba, tunda faɗa ya yi kawai a wurin, sai daga baya za a aiwatar da ko ma menene.
Bayan kwana ɗaya da kammala bikin, wato ranar Litinin kenan, wakilin namu ya tuntuɓi ango Yusuf Saseen don jin abin da Rarara ya bayar na gudunmawar bikin kamar yadda ya furta, sai ya kada baki cikin raha ya ce, “Ai yanzu ni yarinyar nan ta ma fi ni kuɗi; N400,000 su ka ba ta wallahi.”
To, shi kuma nawa ya ba shi kenan? Sai Saseen ya amsa da cewa, “Ni nawa bai iso ba tukunna, amma na san wuyar ta mu haɗu ne da shi ne kawai, zai bayar tunda har ya faɗa.”
Waɗanda su ka samu halartar da dama cikin ‘yan fim, musamman waɗanda su ke da alaƙa da kamfanin ‘Saira Movies’ da masu fitowa a shirin ‘Labari Na’, sun haɗa da Aminu Saira, Rabi’u Rikadawa, Ladidi Tubeless, Sulaiman Bello Easy, Yusuf Bello Ɗanƙundalo, Maryam Yahaya, Yasin Auwal, Maje El-Hajeej Hotoro, Sani Mai Iyali, Yakubu Muhammad, Al-Amin Ciroma, Abdul Amart, Hadiza Kabara, Rabi’u Liba, Hadizan Saima, Hadiza Maikano, Nazifi Asnanic, Samha M. Inuwa, Murja Ibrahim Kunya, Ummi Gayu, Ezet Edita, Asma’u Wakili, Bashir Abdullahi El-Bash, Nasir Naba, Hassana da Hussaina na ‘Daɗin Kowa’, Ahmad Bello (Nazir a ‘Daɗin Kowa’), Maryam Bakasee da dangin amarya da su ka zo daga Potiskum da kuma wasu daga cikin shahararrun ‘yan TikTok, mazan su da mata.

An yi ta zuba ido don ganin Naziru Sarkin Waƙa, amma har aka tashi daga taron da misalin ƙarfe 11:30 na dare ba a ga ko ƙeyar sa ba. Hakan ya jawo ƙananan maganganu daga wasu mahalarta taron kan dalilin rashin zuwan nasa.
An dai gudanar da taron lafiya an kuma tashi lafiya, sannan amarya ta tare a gidan mijin ta da ke Kano.
Da fatan Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.



Comments 3