• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Aisha Tsamiya: Ba gobe zan yi aure ba, sai nan gaba

by DAGA ABBA MUHAMMAD
February 24, 2022
in Ranar Murna
1
Aisha Aliyu (Tsamiya) ta ce sai a watan gobe za a yi auren ta

Aisha Aliyu (Tsamiya) ta ce sai a watan gobe za a yi auren ta

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

BAYA ta haihu. Fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya) ta bayyana cewa ba a gobe Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 ba ne za a ɗaura mata aure kamar yadda aka yaɗa a soshiyal midiya.

Wannan sabuwar sanarwar ta biyo bayan yaɗa wani katin gayyatar aure ne wanda aka yaɗa a soshiyal midiya, ana cewa na auren jarumar ne.

A katin, an nuna cewa fitacciyar jarumar za ta yi aure a ranar Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022.

A katin, wanda mujallar Fim ta gani, an bayyana sunan sahibin nata, wato Alhaji Buba Abubakar, kuma aka ce za a ɗaura auren da misalin ƙarfe 1:00 na rana a masallacin Sheikh Zarban da ke Kwanar ‘Yanwanki, kusa da gidan Tanko Yakasai da ke unguwar ‘Yankaba, a Kano.

Tun da labarin auren ya ɓulla a soshiyal midiya abokan sana’ar A’isha su ka shiga yi mata fatan alheri, inda kusan dukkan su sun ɗora hoton ta tare da katin auren.

To amma ɗazu ɗazun ban Aisha Tsamiya ta hau Instagram ta rubuta cewa, “Assalamu alaikum, jama’a barkan mu da warhaka. Na gode da addu’o’in ku da fatan alkhairi, na ji daɗi sosai, amma aure na ba 25th ga wannan watan ba ne, sai next month in-sha Allah……Na gode Allah ya saka da alkhairi.”

Sanarwar Aisha Tsamiya a Instagram

Wannan sanarwar, wadda Tsamiya ta yi a shafin ta na Instagram mai mabiya sama da miliyan ɗaya, ya ba mutane da dama mamaki.

A’isha Tsamiya dai ta na ɗaya daga cikin jaruman Kannywood da wasu ke ganin kamar sun ƙi aure ne.

Wasu kuma su na yi mata kallon mayaudariya, don su na cewa akwai lokacin da ta yaudari darakta Mu’azzam Idi Yari da kuma jarumi kuma mai bada kayan sawa (costumier) Sadiqu Atis.

Haka kuma a ‘yan shekarun baya har an gama maganar auren ta da wani attajiri da ke Jihar Kebbi, wanda aka sa bayan ta dawo daga aikin Hajji za a yi bikin, ta na dawowa sai kuma labari ya canza, aka fasa auren. Wasu na cewa ita ce ta ce ta fasa auren, yayin da wasu su ka riƙa cewa shi ne ya fasa saboda wasu dalilai.

Kafin wannan lokaci, an ɗauki tsawon lokaci ba a jin ɗuriyar jarumar a Kannywood, musamman a yanzu da masana’antar ta koma cin kasuwa a YouTube. 

Mujallar Fim ta lura da cewa jarumar ta duƙufa ne wajen kasuwamcin ta; da ma ta daɗe da buɗe shagon saida kayayyakin sawa na mata, takalma, dogayen riguna da sauran su.

Wakilin mu ya yi ta ƙoƙarin kiran ta a waya don jin yadda shagalin bikin zai kasance da kuma abin da za ta ce wa masoyan ta da kuma jin wanene angon nata, da inda su ka haɗu da sauran su, amma kuma hakan bai yiwu ba, don ba a samun ta a waya.

Katin auren Aisha Tsamiya da aka yaɗa

Loading

Tags: Aisha Aliyu TsamiyaBuba Abubakarɗaurin aurehausa filmsKannywoodMu'azzam Idi Yari.Sadiqu Atis
Previous Post

Abin ya zo! Za a ɗaura auren jarumar Kannywood Hassana Muhammad da furodusa Bashir Maishadda

Next Post

An ɗaura auren Aisha Tsamiya duk da iƙirarin da ta yi cewa wai sai nan gaba

Related Posts

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Next Post
Amarya Aisha Tsamiya da angon ta Buba Abubakar

An ɗaura auren Aisha Tsamiya duk da iƙirarin da ta yi cewa wai sai nan gaba

Comments 1

  1. Pingback: Aisha Aliyu Tsamiya Ta fitar da sanarwa akan Aurenta – HausaLoaded.Com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!