• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar minista Sadiya ga ɗaliban shirin ‘N-Build’ 40,000 da aka yaye: Horaswar da ku ka samu za ta taimaki rayuwar ku a ko’ina

by DAGA IRO MAMMAN
June 9, 2022
in Nijeriya
0
Minista, Hajiya Sadiya Umar Farouq, na miƙa satifiket da kayan aiki ga wata naƙasasshiya da aka ba horaswar yin sana'a

Minista, Hajiya Sadiya Umar Farouq, na miƙa satifiket da kayan aiki ga wata naƙasasshiya da aka ba horaswar yin sana'a

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAR Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ta bayyana cewa horaswar da aka ba ɗaliban shirin ‘N-Build’ kashi na ‘C1’ za ta amfane su a tsawon rayuwar su, kuma a duk inda su ka shiga.

Ministar ta bayyana haka ne a wajen bikin yaye ɗaliban da su ka ci gajiyar shirin, kashi na ‘C1’, wanda aka yi a ranar Laraba a Abuja.  

An yi watanni uku ana horas da waɗanda su ka shiga tsarin, wanda aka yi a ƙarƙashin shirin nan na Gwamnatin Tarayya na inganta rayuwar ‘yan Nijeriya, wato ‘National Social Investment Programme’ (NSIP) da kuma shirin ‘N-Power’.

A wajen bikin, ministar ta kuma raba kayan aiki ga dukkan waɗanda aka yaye a wata makarantar koyar da sana’o’i mai suna ‘FOCI Skills Academy’ da ke unguwar Katampe a Abuja.

A taron, Hajiya Sadiya ta yi la’akari da cewa wannan horaswa ko tirenin da aka yi, an yi irin sa a wasu cibiyoyi har 693 a faɗin ƙasar nan da nufin ƙarfafa wa matasan da ba su da aikin yi gwiwa domin su samu ƙwarewar yin sana’a da za ta taimaki rayuwar su.

Minista Sadiya tare da wasu matasa da aka yaye bayan an horas da su

Ta ce masu, “Ƙwarewar da ku ka samu wajen horaswar a watanni uku da su ka gabata za ta kasance muhimmiyar hanyar da za ta taimake ku a yau da kuma gobe a kowane tsarin tattalin arziki na duniya. 

“Wannan ma’aikata, tare da shugabannin gudanar da shirin NSIP da ‘N-Power’ da sauran cibiyoyin da abin ya shafa, sun yi aiki tuƙuru don tabbatar da  cewa wannan abu ya taimaka wajen rage buƙatar da ake yi ta ƙwararrun da aka horas don ɗaukar su aiki.

“A wannan aji na ‘C1’ na shirin ‘N-Build’, an yaye ɗalibai ne domin su fara zama ƙarƙashin wasu masu irin sana’ar su, kamar yadda mai girma Shugaban Ƙasa ya ƙudurci samar da ƙarin ayyukan yi da hanyoyin samun arziki ga ɗimbin matasa. Za a tura su zuwa wurare daban-daban inda za su fara ayyukan su. 

“Sannan su ma ‘yan aji na C2 na shirin ‘N-Power’, nan da makonni kaɗan za a tura su cibiyoyin horaswa, wanda duk manufar dai ita ce a tsamo ‘yan Nijeriya miliyan 100 daga ƙangin fatara.”

Ministar ta bayyana cewa an sama wa kowanne daga cikin masu cin moriyar shirin ƙunshin kayan aiki da kayan tsaron lafiyar jiki a wajen aiki, da kayan zuwa wajen horaswa don a ba su damar yin aiki a matsayin ƙwararrun masu sana’a da aka horas.

Ta yi kira a gare su da su yi amfani sosai da horaswar da aka ba su.

Hajiya Sadiya ta ce: “Tunda har kun gama horaswar cikin gida, za a haɗa ku kai-tsaye da hukumomin da su ka dace domin zaman koyo da za ku yi da su na tsawon wata shida. 

“Wannan zaman koyon zai ba ku damar samun ilimin aiki, wanda za a fara shi daga ranar Litinin, 13 ga Yuni, 2022. 

“A lokacin wannan zaman koyon na watanni shida, za a duba aikin ku tare da auna shi, wanda Cibiyar Magina ta Nijeriya Mai Rajista (Council of Registered Builders of Nigeria, CORBON) da Cibiyar Tsara Kayan Ƙirƙira ta Ƙasa (National Automotive Design and Development Council, NADDC) da kuma Hukumar Ƙwararru ta Masu Aikin Yawon Shaƙatawa ta Nijeriya (Institute of Tourism Professionals of Nigeria, ITPN) su za su yi maku.”

Ɗaliban da aka yaye ɗin dai sun samu horo ne a fagagen gyaran mota, fasahar aikin gona, aikin kafinta, aikin haɗa wutar lantarki, aikin gini da sa tayil, aikin famfo da shimfiɗa fayif.

Haka kuma ministar ta je Gidauniyar Cibiyar Masana’antu (Industrial Trust Fund Centre) domin miƙa ƙunshin kayan aiki da kayan fara sana’a ga ɗaliban da aka yaye a fagen sana’ar yawon buɗe ido, waɗanda su ka haɗa da koyon tuya da haɗa alawa, dafa abinci, kula da gida da kimtsa shi, da kuma dabarun haɗa abin sha.

Waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala, da Darakta-Janar na Hukumar Magina ta Ƙasa (Federation of Construction Industry), Mista Olubunmi Adekoje, da Babban Kodineta na Shirin NSIP, Dakta Umar Bindir, da shugaban masu aiwatar da shirin ‘N-Power’, Mista Nsikak Okon, da sauran manyan baƙi.

Loading

Tags: agajiFarfesa Kabir BalafataraFOCI Skills AcademyhoraswaHumanitarian Affairsinganta rayuwaN-BuildN-PowerNISPNsikak OkonpovertySadiya Umar Farouqsana'o'iskillsUmar Bindir
Previous Post

Ya yi ƙarar jarumar Kannywood Hadiza Gabon a kan zargin ta ci masa kuɗi ta ƙi auren sa

Next Post

Zaɓen 2023: INEC ta bayyana ranakun rufe karɓar sunayen ‘yan takara

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Farfesa Mahmood Yakubu

Zaɓen 2023: INEC ta bayyana ranakun rufe karɓar sunayen 'yan takara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!