FITACCEN jarumi Musa Maisana’a ya ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake bazawa cewa wai ‘yan sanda sun kama shi saboda ya jagoranci sallar Juma’a a Kano.
A yau da yamma ne dai labarin ya riƙa yawo a kafofin soshiyal midiya.
Da farko dai labarin cafke Maisana’a ya fara kamar wasa, amma zuwa ɗan wani lokaci sai ya cika gari.
Domin jin haƙiƙanin yadda abin ya ke ne mujallar Fim ta tuntuɓi jarumin ta waya, inda shi kuma ya ce labarin ba gaskiya ba ne.
A cewar sa: “Wannan labarin ba gaskiya ba ne, domin ni ba malami ba ne, kuma ba ni da wani masallaci da na ke jan sallah.
“Don haka wasu ne dai kawai su ka haɗa labarin don wata manufa. Amma dai maganar gaskiya, ba a kama ni ba.
“Don yanzu maganar da mu ke yi da kai idan ka na son mu haɗu da kai sai ka faɗa mini duk inda ka ke na zo na same ka don ka tabbatar da gaskiyar maganar, don haka ina nan.
“Ban yi wani laifi da har za a kama ni ba. Ni mai bin doka ne, don haka babu yadda za a yi na samu kai na a cikin masu ƙin biyayya da abin da hukuma ta zartar domin neman maslahar jama’a.”
Sanin kowa ne cewa gwamnati ta kafa dokar zaman gida sakamakon annobar cutar korona mai kisa.
Alƙaluma na baya-bayan nan sun nuna cewa cutar korona na daɗa yaɗuwa ne a faɗin Nijeriya.
Hukumar yaƙi da cututtuka ta ƙasa (wato Nigeria Centre for Disease Control, NCDC) ta bayyana cewa cutar ta kama mutum 381 a faɗin Nijeriya a jiya Alhamis, cikin su har da mutum 55 a Kano.
Hakan ya sa an samu jimillar mutum 3,526 da su ka kamu a Nijeriya.
Mutum 107 ne su ka mutu zuwa yanzu.