• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Cewar Rarara a taron 13×13: Za mu iya ciyar da mutum miliyan goma idan mun haɗa kai

by DAGA ABBA MUHAMMAD
May 12, 2022
in Labarai
0
Dauda Kahutu (Rarara) ya na gabatar da jawabi a taron

Dauda Kahutu (Rarara) ya na gabatar da jawabi a taron

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

SHUGABAN ƙungiyar matasan Kannywood ta 13×13, Alhaji Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya bayyana cewa sai an haɗe an zama ɗaya ne ƙungiyar za ta yi irin tasirin da ake so ta yi.

Ya faɗi haka ne jiya Asabar, 21 ga Mayu, 2022 lokacin da ƙungiyar ta 13×13 ta yi taron rarraba masara da kuɗi ga dukkan ‘ya’yan ƙungiyar.

Shi ne taron ƙungiyar na farko bayan an dawo daga hutun Sallah.

Taron, wanda aka shirya cewa za a gudanar a ɗakin taron nan mai suna Meena Event Centre, Kano, daga baya aka sake sanarwa cewa an canza wurin taron zuwa Izeema Events Centre da ke Titin Magaji Rumfa, a Kano. 

An fara taron da misalin ƙarfe 12:00 na rana bayan isowar shugaban ƙungiyar, wato Rarara. 

Bayan fitaccen jarumi Malam Isa Bello Ja ya buɗe taro da addu’a, sai Rarara ya yi jawabi a kan dalilin kiran taron, inda ya ce, “An gabatar da jawabai iri-iri, kala-kala waɗanda su ka shafi 13×13, musamman garkuwa da aka yi magana na Baba Buhari, Malam Nura M. Inuwa, wanda in Allah ya yarda akwai baitin shi wanda za mu ƙara maimaitawa, in-sha Allah. 

“An ce in tattara  maganganu in su ni kaɗai don an daɗe ana jira. Akwai maganganun mutane da yawa a nan wurin kowa sai na masa tashi.

“Don Allah jama’a a yi haƙuri na rashin zuwa wurin wannan taro da wuri. Wannan haɗuwa Allah ya ƙara wa abin albarka don da ma mai albarka ne.

Wani ɓangare na membobin 13×13 su na sauraren jawabin Rarara

“Mun dai haɗu a nan wurin don in gabatar da wani saƙo wanda ya kamata a ce tun ranar Sallah ko washegarin Sallah mu ka yi. Ba mu yi ba saboda duk yawanci mu na wurin hidimomin Sallah, kuma waɗanda ya kamata mu kira ɗin su ma su na da nisa, don akwai Kebbi, akwai Maiduguri, ka ga idan na ce haka na ƙure Nijeriyan kenan.

“Abu na farko da saƙo ne mu ka samu daga ƙungiyar ‘Buhari For All’ na kayan da ake kira ‘Ramadan Kareem’. Mun karɓi saƙon nan, in Allah ya yarda duk wanda ya ke cikin ƙungiyar nan zai ji shi, zai taɓa shi, shi ma zai ci. To in Allah ya yarda ga wannan saƙo mun zo da shi.

“Sai kuma magana ta biyu da ya kamata in yi, jadawalin wannan ƙungiya ko kuma turakun ta, don shi ne a kan sana’ar mu mu ke so mu tsaya. 

‘Mu na so mu tsaya a kan ƙafafun mu, shi ya sa mu ka ɗauki layi ɗaya zuwa biyu, layi na ukun da ƙyar aka ɗauke shi, don a kan shi ma na so na rasa kujera ta, shi ne maganar siyasa. 

“Mun ɗauki layin tunda dai yawanci mu mutane ne masu motsi; ma’anar masu motsi, maganar mu kuɗi, fuskar mu kuɗi, rawar mu kuɗi, tafiyar mu kuɗi, bai kamata a ce sai mun tsaya mu na dogara da wani ya ba mu wani abu ba, mu ne ya kamata mu bayar. 

“Mu na zuwa gidan marayu, mu na zuwa gidan yari, mu na zuwa maida yaro makaranta, mu na zuwa mu kai tallafi asibiti, mu na son yi wa ƙungiyar tamu garambawul ko kuma masana’antar mu a ce mun iya tsayawa da ƙafar mu, ya zamanta fim ɗin da za a yi shi a Bollywood za mu iya yin shi a nan, fim ɗin da za a iya yin sa a Hollywood za mu iya yin shi a nan. 

“Wannan ba zai yiwu ba in ba haɗewa mu ka yi ba. Mutum goma idan su na da kuɗin da za su yi fim kowa nashi, to a haɗe a yi guda ɗaya ƙwaƙƙwara, wanda zai zama makusancin ɗari a abin da za a samu a kan shi. Shi ne wanda za ka iya gani a Netflix; duk duniya inda ake kallon fim za a ce wannan fim ya cancanta. 

“In ba mu haɗe ba wannan abin ba zai iya yiwuwa ba.

“Ina ganin maganganun da zan iya yi kenan guda uku. Na farko na yi maganar ƙungiya, an samu tallafi daga ‘Buhari For All’ na shinkafa rabin mota, masara mota ɗaya. Waɗannan kaya ga su mun zo da su nan wurin, an yi lissafi. 

“Malam Abu Maishadda, sakataren ƙungiya kuma minista na bojet da tsare-tsaren mu  da shi kuma Yakubu Mohammed, shugaban tsare-tsare, an ƙiyasta kowa duk wanda ya ke cikin 13×13 na jihohi kowa zai samu buhu uku na shinkafa, buhu huɗu na masara, kowa zai tashi da buhu bakwai kenan. 

“Wanda bai zo ba za a kai masa wannan saƙo har gida. Kuma akwai N20,000 da za a ba wa kowa, wanda bai zo ba saƙon zai isa wurin sa. 

“Shi ya sa mu ka ce mu zo da wakilai, kuma mun aminta da wakilan su za su kai masu wannan saƙo. 

“Abin da ya sa na fara da wannan shi ya fi nauyi, saboda nauyi ne aka ce an ba ƙungiya, ya kamata mu sauke shi. 

“Sai kuma maganar da ta shafe mu ta kan mu shi ne ya fi komai a cikin wannan ƙungiya ko kuma a cikin wannan masana’anta. Alhamdu lillahi mun ɗauki layi, mun ɗauki matsaya  za mu tsaya a kan ƙafar mu, in-sha Allahu. Ko da haɗe-haɗen kuɗi ne za  mu yi da zai riƙe mu, ya riƙe masana’antar mu da ma ƙungiyar mu, in-sha Allahu. Shi ne maganar akwai harkar wasanni da mu ka tsara,  za mu iya yin aiki a biya mu, za mu iya amsar kwangila mu yi a ƙungiyance. 

“Wannan shi ne jadawalin da aka ɗauka wanda zai riƙe wannan ƙungiya, in-sha Allahu. Mun san zai iya, saboda a nan mutun ɗaya zai iya ba mutum hamsin abinci, mutum ɗaya na iya ba mutum goma abinci. To ka ga in mu ka ce za mu haɗe kan mu mu yi abubuwan nan, wurin mutum miliyan goma za su iya cin abinci ta ƙarƙashin wannan ƙungiyar, in-sha Allahu. 

“Sai kuma tsari na 13×13 na jadawalin kowa. Kowa ya na da shinkafa buhu uku, masara buhu huɗu da kuma N20,000 da za a ba kowa. Duba da ita yanayin ƙungiyar, bai kamata a ce mutum ya zo daga wuri mai nisa ba a ce ya koma haka, shi ya sa aka yi tunanin samar wa mutane wannan ɗan abin hasafi. 

“Magana ta kusa da ƙarshe, maganar da ya kamata in yi, wannan kwamiti na ne na harkar waƙe-waƙe da nema wa gida mafita. Wannan kwamiti an yi waƙoƙi da yawa, su na nan an tutturo za mu fara zama in Allah ya yarda sati na sama, wato bayan ‘primaries’ kenan, saboda waɗanda za mu gani ɗin duk hankalin su ba ya kan abubuwa, dole sai kowa ya san ina ne matsayin shi. 

“Saboda haka in Allah ya yarda sati na sama za mu bada lokaci za a zauna a tantance waƙoƙin, waɗanda ya kamata su tafi ‘direct’ da kuma waɗanda ya kamata mu canza masu yanayi da kuma waɗanda ya kamata mu bada gyararraki domin tafiyar ta tafi yadda ake buƙata.

“Mu na kuma fatan Allah ya ba mu sa’a. Kuma a yi mana addu’a game da wannan kwamiti namu, don kwamiti ne wanda ya ke so ya samu, ya kuma sama wa waɗanda su ke ciki insha Allahu.

“Mu na kuma da maganganu guda uku, waɗanda za mu yi taro na kwana biyu ko uku shi ne na ɗaukar matsaya a kan maganar takarar shugaban ƙasa da gwamnoni. Shi ya sa mu ka ce don Allah duk wanda ke ƙungiyar nan in ya na da maigida ba mu hana shi mu’amala da shi ba, amma dai mu yi ‘hanging around’ don ƙila za mu iya zuwa mu ɗauki layin da ba maigidan ka ya ke ba. Kuma dole za ka yi mana kara don shi ne mu ma za mu iya yi maka. Karar ita ce guda biyu, ko dai ka yi mana hanyar da za mu zauna da maigidan ka mu shiga cikin tafiyar sa gadan-gadan ya yi mana alƙawuran da zai yi mana, kuma ya ba mu iya abin da za mu iya karɓa na wanda za mu taya shi aiki. In Allah ya sa an kai gaci alƙawari ya cika. 

“Ko kuma mu zo maka da namu, ka aje naka, mu runguma mu tafi. Wannan maganar ta fi ƙarfi a kan ‘yan jihohi. Babu maganar PDP ce ko APC ce ko mai kayan marmari ko APGA ko wani abu dai. Mu mu na maganar mafitar ƙungiyar nan ne; duk abin da  za mu yi mafitar masana’antar mu shi mu ke nema.

“Saboda haka idan buƙatar mu ta fi taka, za ka haƙura da taka, za ka ɗauki tamu. Kuma inda mnaganar ta fi ƙarfi a kan takarar shugaban ƙasa da kuma gwamna, duk maganar sanata ko ɗan majalisa za mu yafe maka. 

“Amma dai a maganar shugaban ƙasa da gwamna mu nan mu na duba na tsanaki mu ga ina ya kamata mu yi, saboda akwai ‘yan takarkari sun fito da yawa birjik, amma dai babu inda mu ka ce mun yi nan, sai mun zauna da waɗanda su ka kira mu ko su ka nemi mu zauna mu ji manufar ka ta maganar ƙasar nan, musamman a kan abin da mu ke ciki yanzu na matsalar tattalin arziƙi da sha’anin tsaro, saboda shi ne ya ke ruhin sana’ar mu. Idan tsaro, sana’ar mu ta na cikin shirmuci, ta na cikin tasgaro da damaga. Sai mun samu tsaro za mu iya zuwa mu yi shutin, saboda gudun shirmuci.

“Saboda haka akwai ‘yan takarkaru da su ka fito waɗanda mu na nan mu na dubawa mu gani, mu ga in za mu yi tallar su ta ya za mu yi, za mu iya? In ba za mu iya ba dole mu haƙura mu ɗauki inda za mu iya yi. Ita nasara ta na wurin Ubangiji. 

“Magana ta ƙarshe, mutanen mu na 13×13 waɗanda su ke cikin zagaye da ma na jihohi, gaskiya mun tsara wasan Sallah,  wanda akwai Gombe, Kano,  Maraɗi da Yamai. Wannan kwamiti ya na aiki da yawa, shi ya sa kwamitin ya kawo kuka a gida ya don Allah, don Annabi musamman wasu  su na nan wurin, kada su karɓi wasan Sallah, saboda wannan karon mun yi ƙarya mun ce wane zai zo, wane zai zo, an zo an samu matsala, an samu tasgaro a cikin hidimar. 

“Yanzu ma mu na magana da wani, wai ya yi alƙawari Cote d’Ivoire. Wannan alƙawarin 13×13 ta goge shi, kuma an sa hannu. 

“Akwai mutanen mu da za mu yi ‘oromoting’, akwai waɗanda za mu girgiza su, da ma su su na nan. Da ma in an haɗu wuri ɗaya ne wani ke tashin wani, waɗanda su ka karɓi wasu don Allah, don Annabi su ba masu wasannan haƙuri mu na da wasa, in su na so su kalli mutum ne su je Maraɗi, zai je Yamai, ƙila za mu haɗu a Doso. 

“A waɗannan garuruwan za mu yi wasa in Allah ya yarda. Jadawalin an tsara, idan aka yi ‘posting’ a guruf duk wanda ya ga sunan shi zai ga inda aka tura shi wasa da kuma inda zai ƙarƙare. 13×13 ta yi wannan shiri, saboda wannan ya na ɗaya daga cikin jijiyoyin wannan ƙungiya domin dogaro da kai. 

“Mu na magana da kamfanoni da yawa waɗanda za su shiga cikin hidimomin nan waɗanda za su ɗauki nauyi, mu kuma za mu yi masu talla. 

“Sannan akwai kwamitin lafiya wanda Nura M. Inuwa shi da Abale ke jagoranta; su ma za su yi aiki a sati mai zuwa. 

“Akwai asibiti da za su je kamar guda biyu. An yi odar ledar ruwa amma ba su ƙaraso ba, akwai ledar jini da safar hannu. 

“Akwai kuma kwamitin da ‘Women Leader’ ke jagoranta, Hajiya Saratu Giɗaɗo (Daso). Akwai makarantun mata, za mu kai ziyara mu bada tallafi. Idan waɗanda za su iya biyan ‘admission’ sun biya, za mu ba su tallafi wanda za su ci gaba da karatu ko da iyayen su ba su aiko masu da wani abu ba. 

“Wannan ɓangaren dole Daso sai ta aje komai nata ta rungumi sauran matan sun tafi wurin wannan aiki, tunda da ma ta ce aikin Allah za ta yi. 

Buhunan shinkafa da madara da aka raba

‘A ƙarshe, ina yi wa dukkanin waɗanda su ka zo fatan alheri, kuma yadda kowa ya zo lafiya Allah ya maida ku gida lafiya.”

Bayan Rarara ya ƙarƙare jawabin sa, sai kuma aka shiga maƙasudin kiran taron. An umarci kowane memba na ƙungiyar da ya samu jagoran sa don karɓar saƙon sa.  

Abubakar Bashir Maishadda da Yakubu Muhammad ne su ka jagoranci rabon baki ɗaya.

Ƙungiyar 13×13 dai ƙungiya ce ta mutum sha uku, kuma kowane mutum ɗaya a cikin sha ukun ya na da mutum sha uku da ke ƙarƙshin sa.

Manya da ƙananan jarumai da ke cikin ƙungiyar sun halarci taron. Kuma kowa ya tashi da buhun shinkafa uku da buhun masara huɗu, haɗe da N20,000.

Loading

Tags: 'Buhari For All'Abubakar Bashir MaishaddaDauda Kahutu RararaKannywoodKanokungiyar 13x13Ramadanzaben 2023
Previous Post

Zaɓen 2023: Zan yi aiki tuƙuru wajen ƙarfafa nagartar Jihar Neja – Malagi

Next Post

A taimake ni ‘ya’yan Sarkin Kano za su halaka ni, cewar matar Ɗandarman Kano Hauwa Bello Ado Bayero

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Hajiya Hauwa Bello Ado Bayero

A taimake ni 'ya'yan Sarkin Kano za su halaka ni, cewar matar Ɗandarman Kano Hauwa Bello Ado Bayero

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!