KAFIN cutar ‘Coronavirus’, an yi cututtuka masu yaɗuwa da dama waɗanda su ka samu tallar kafafen yaɗa labaran duniya matuƙa. Misalin cutukan su ne: Kwalara, ‘HIV/AIDS’, ‘Ebola’, ‘Lassa Fever’, ‘SARS’, ‘Anthrax’, kai har da ma na dabbobi dangin su ‘Bird Flu’ da ‘Swine Flu’. Dukkan waɗannan cutuka, waɗanda aka ambata da waɗanda ba a ambata a nan ba, akasarin su sun zo, kafafen labaran duniya sun yayata, jama’ar duniya ta firgita ainun, gwamnatoci kuma sun kashe maƙudan kuɗaɗe don rigafi ko warkar da cutukan.
A lura, manufar rubutun nan, ba don ƙaryata cutukan ba ne, a’a, domin fitar da wasu ababen hankalta ne waɗanda marubucin nan ke fatan su ƙarfafi zuciyar mai karatu a wannan yanayi da ake ciki.
Cutuka masu yaɗuwa dai ba ƙarya ba ne, an yi su ko akwai su. Amma abin da akasari ba su sani ba, ko kuma sun sani amma su na shakkar yiwuwar sa shi ne, bunƙasar ilimi ya sa ana iya ƙirƙirar cuta don cimma manufar samun kuɗi ko don cimma manufar siyasa ko duka biyun. Waɗanne masu ilimi ne ke ƙirƙirar cuta don su amfana haka? Su ne waɗanda a zahiri su ke amfana daga yaɗuwar cutar. Binciken wannan, na mai karatu ne.
A ranar 19 ga Disamba ta shekarar 2017, CNN ta wallafa rahoton wani wakilinta, Wayne Drash, mai taken: “Investigating the World’s Deadliest Diseases”. Faƙarar farko da ta biyu na rubutun sun haskaka wannan batu na ƙirƙirar cutar da cewa:
“The US government on Tuesday lifted a ban on making lethal viruses, saying the research is necessary to develop strategies and effective countermeasures against rapidly evolving pathogens that pose a threat to public health.
“Dr. Francis Collins, director of the National Institute of Health, made the announcement, in which he outlined a new framework for the controversial research. The work with three viruses can now go forward, but only if a scientific review panel determines that the benefits outweigh the risks.”
Ma’ana: “A ranar Talata gwamnatin Amurka ta ɗage dokar hana ƙirƙirar muggan cutuka masu yaɗuwa, ta na mai cewa cigaba da binciken a kan su wajibi ne don zai bunƙasa dabaru da hanyoyin ƙalubalantar sinadaran cutuka masu haɓaka waɗanda su ke barazana ga lafiyar jama’a.”
Kafar ta CNN ta cigaba da cewa: “Dakta Francis Collins, daraktan Hukumar Lafiya ta Ƙasa, ya shaida haka, inda ya fitar da wani sabon tsari a kan binciken da ake taƙaddama a kai. A yanzu za a cigaba da aikin samar da cutukan uku masu yaɗuwa, amma fa sai kwamitin masu nazarin kimiyya ya tabbatar da cewa amfanin da za a samu sakamakon cigaba da binciken ya fi hatsarin da za a fuskanta.”
A cikin wannan rahoto, mai karatu zai fahimci cewa da gaske manyan gwamnatocin duniya su na ƙirƙirar cutuka masu yaɗuwa. Sai dai dalilin ƙirƙirar kuma wani turanci ne da ake son yi wa jama’a wayon sa.
A shafin YouTube, akwai wani shiri mai taken: “Engineered Viruses Are the New Biological Weapons: Here is What You Need to Know.” A ciki, an nuna yadda masana kimiyya su ke sanya wasu sinadarai a abinci dangin biredi waɗanda su ke canza hatta tsarin halittar ɗan’adam, wato DNA. Haka nan an nuna yadda su ke ƙirƙiro cutukan nan masu yaɗuwa da ake kira “viruses” a matsayin makamai na kisa. Hakazalika an nuna hoton shafin jaridar ‘New York Times’ inda ta yi wani rahoto a shafin ta na farko mai taken: “Scientists Create A Live Polio Virus”, ma’ana: “Masana Kimiyya Sun Ƙirƙiro Rayayyiyar Cutar Foliyo Mai Yaɗuwa.”
Mista Thabo Mbeki, tsohon shugaban Afirka ta Kudu, ya zargi Amurka da alhakin ƙirƙirar cutar ƙanjamau (AIDS), ya ce a ɗakin ƙera magani na sojan Amurka aka ƙirƙiro ta.
Ita ma mashahuriyar masaniyar ilimin dabbobi da tsirrai, ‘yar ƙasar Kenya, Dakta Wangari Maathai, ta shaida wa duniya a zauren taron lambar yabo na ‘Nobel Peace Prize’ da aka ba ta cewa:
“AIDS is not a curse from God to Africans or the Black people. It is a tool to control them designed by some evil-minded scientists.”
Ma’ana: “Cutar AIDS ba bala’i ce daga Allah zuwa ga ‘yan Afirka ko Baƙar Fata ba. Dama ce ta mallakar su, wadda wasu mugayen masana kimiyya su ka ƙirƙira.”
Haka zalika Rev. Jeremiah Wright, tsohon malamin Barack Obama na addinin Kirista wanda aka sani da tsage gaskiya, ya ce:
“Inventing the HIV virus was a means of genocide against people of color.”
Ma’ana: “An ƙirƙiri cutar HIV ne don kisan ƙare dangi ga mutanen da ba fararen fata ba.”
An ce ire-iren waɗannan zantuka ne su ka raba shi da tsohon shugaban Amurkan, Barack Obama.
Zantukan waɗannan mutane uku sun janyo masu Allah-wadai daga masu faɗa-a-ji na duniya. Sun tashi daga matsayin su na masu farin jini sun zama masu baƙin jini domin abin da su ka furta da bakin su. Sai dai kuma abin mamaki, har zuwa yau ɗin nan ba a samu wani gamsasshen bayani da ya ƙaryata da’awar tasu ba. Kawai dai an kira abin da su ka ce da ƙirƙirarren tunani ne (“conspiracy theory”). To shin, ita da’awar cewa cutar AIDS ta fara daga birai ne a 1930 ba ƙirƙirarren tunanin ba ne? Wane binciken kimiyya ya tabbatar da haka in ban da cewa an faɗa da fatar baki kuma kafafen yaɗa labaran Turai sun yayata? In kuma akwai binciken, a nuna wa duniya yadda aka gudanar da shi mana.
Idan ma wannan dalilin na su Dakta Wangari Maathai bai zama don rage adadin wani jinsi ba a haƙiƙa, abin da ya zahirta ɓaro-ɓaro shi ne kamfanonin Turai sun fi kowa cin gajiyar yamaɗiɗin cutar AIDS da ake yi ta hanyar samun ƙazamar riba daga ƙera robar kwandom na rigafi, da ƙera magungunan da wai su ke kira na ririta cutar ne waɗanda su ke sayar wa gwamnatocin ƙasashe masu tasowa a kan biliyoyin daloli.
Wannan shi ne misalin yadda ake ƙirƙirar cutuka domin cimma muradai na siyasa ko na neman kuɗi. Cutar ‘Corona’ ma na cikin waɗannan cutuka. Saboda tun ba a je ko’ina ba, kafafen yaɗa labarai na Turai sun fara zaɓe da yaɗa labaran siyasar durƙusar da haɓakar ilimin kimiyya ko tattalin arziƙin ƙasashen da ba ‘yan ɓangaren su ba.
Ga wasu misalai a gurguje, don na san ni da ku (masu karatu) zuwa yanzu duk mun gaji:
Daga ranar da aka ce cutar ta ɓulla a Chaina, kafafen yaɗa labarai na Turai su ka yi ta kai gwauro su kai mari wurin baƙanta fuskar ƙasar. A garin da cutar ta ɓulla, akwai kimanin mutum miliyan 12, amma yadda aka riƙa bada labarin, kai ka ce rubu’in mutanen ƙasar ne ma su ka mace alhali adadin waɗanda su ka mutun bai kai dubu uku ba har zuwa yau. Chaina ta yi ƙoƙari ta daƙile farfagandar labaran da gina katafaren asibitin warkar da cutar a cikin mako guda tal. Amma ƙiri-ƙiri wannan bajinta ba ta samu yamaɗiɗin da ɓullar cutar ta samu ba. Daga nan ma, sai kafafen su ka maida cocilar zaƙular labaran su ga ɗaiɗaikun mutanen da su ka mutu. Su ka riƙa ruwaito cewa likitocin da ke ƙoƙarin kwantar da cutar ko warkar da ita su ma sun mutu. Kimanin mutum 20 cikin su. Har ma da shugaban su baki ɗaya.
Wannan dabara ce ta firgitarwa, don nuna wa duniya cewa Chaina, duk da bunƙasar ilimin kimiyya da fasahar ta da duniya ta shaida, ba ta da ƙarfin da za ta tunkari cutar.
Haka ma su ke wa Iran a yanzu duk da ta na ta cewa ta fara warkar da marasa lafiyan. Har ma ta ce mutanen Iraƙi da su ka kamu da cutar su shigo asibitocin Iran akwai magani. Amma kafafen yaɗa labarai na Turai rahoto kawai su ke badawa cewa wane ya rasu a dalilin cutar a Iran, ko an rufe masallaci saboda cutar. Sun ce Iran ce ta ke da mafi munin labari na cutar, amma fa waɗanda su ka kamu da cutar mutum 139 ne.
Ga kuma ƙasar Italiya can ta na fama da waɗanda su ka kamu mutum 400 amma kafafen cewa su ke yi Italiya na ta ƙoƙarin kwantar da fantsamar cutar. Kuma har zuwa jiya da tsakar dare, marubucin nan bai ga wata kafar yaɗa labarai ta Turai da ta ce mutum guda a Italiya ya mutu saboda cutar ba duk kuwa da cewa mutum 400 ne su ka kamu da ita, har ma ga shi ɗayan su ya shigo da ita Nijeriya.
A kasa kunne, daga baya duniya za ta ji yadda kamfanonin maganin Amurka da Turai su ka samar da wani sinadarin lafar da cutar. Sai kuma a yi ta karɓar maƙudan kuɗaɗen gwamnatocin da kafafen yaɗa labarai su ka firgitar a bayan sun naƙasar da ƙima da nagartar kamfanonin ƙasashen da su ke iya bayar da maganin cutar a arahar banza.
Muhammad Bin Ibrahim ɗan jarida ne mazaunin Kaduna