SHUGABAN sabuwar Ƙungiyar Masu Fassarar Finafinai na riƙo, Malam Kabiru Musa Jammaje, ya bayyana cewa an kafa ƙungiyar ne saboda ƙorafin da masu kallon finafinan Hausa su ke yi na rashin inganci a fassarar da ake yi a finafinan.
Jammaje ya faɗi haka ne a lokacin da ya zanta da mujallar Fim a Kano kan manufar kafa ƙungiyar.
A cewar sa, yanzu haka su na ƙoƙarin ganin sun yi wa ƙungiyar rajista da kuma buɗe mata ofishin ta na kan ta.
Tun da farko sai da ya faɗi dalilin kafa ƙungiyar, ya ce, “To ita wannan ƙungiyar ta masu fassara, wato ‘subtitles’, na daɗe ina tunanin yadda za a samar da ita, kuma tun kafin na yi tunanin samar da ita, ‘yan jaridu sun sha hira da ni a kan fassara da ake yi a finafinai da ake yi musu ‘subtitles’ wanda duk wani mai hankali da tunani abin ya na ɓata masa rai.
“Domin na sha haɗuwa da manyan mutane, to sai su ce ina cikin masana’antar ya kuma na bari ake ɓata fassara haka?
“Wannan ya sa na yi ta maganganu a kan a gyara.
“To kuma bayan da Abba El-Mustapha ya zama shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, sai na je na same shi na sanar da shi yunƙurin da mu ke yi na samar da ƙungiyar masu fassarar kuma mu ka nemi goyon bayan sa kuma ya karɓi abin hannu biyu.
“Don haka ma ya ce a cikin kundin tsarin mulkin su da za a gyara har mu a yanzu an saka mu a ciki, saboda haka duk wanda ya zo a nan gaba zai ga akwai ƙungiyar mu a ciki ta masu fassara.
“Don haka wannan cigaba ne aka samu domin babu wata ƙungiya ta masu fassara da aka samar kamar wannan.”

Jammaje ya ƙara da cewa, “Ita ƙungiyar a Kannywood aka samar da ita, amma hakan ba ya na nufin ba za mu iya yin aiki da kowa ba, don haka ko da wasu ƙungiyoyi ne na ƙasashen waje su ke son a yi musu ‘subtitles’ to a shirye mu ke.
“Fassara in dai daga Turanci zuwa Hausa ne ko kuma daga Hausa zuwa Turanci, kai har Faransanci ma zuwa Hausa ko daga Hausa zuwa Faransanci, duk za mu yi. Kuma wannan ƙungiyar ta na da ruwa da tsaki da shi.”
Da mu ka tambaye shi alaƙar su da masu fassara finafinan Indiya kuwa, cewa ya yi:
“Ai su waɗannan su na fassarawa ne da baki, don haka ba sa cikin mu, don mu ƙungiyar mu ta masu fassara ce a rubuce, wato ‘subtitles’, don haka ba mu da alaƙa da su masu fassara Indiya da Hausa, sai dai idan sun nemi su shigo cikin mu mu na maraba da su.”
A game da ƙa’idar ƙungiyar kuwa, cewa ya yi: “A yanzu mu na kan yi mata rajista ne, don haka ba ta gama zama da ƙafafun ta ba. Don haka idan mun gama za mu samar mata da kundin tsarin mulki da kuma wasu tsare-tsare.
“Don haka a yanzu ba a buɗe ta ke ga kowa ba har sai mun gama samar mata da tsari sai mu buɗe ta ga kowa, duk wanda ya ke buƙatar shiga a gabatar masa da dokokin ta wanda kuma a cikin burin da mu ke da shi za mu rinƙa yin bita da taron ƙara wa juna sani.
“Don haka za ta kai matakin da duk wanda zai shiga sai an gwada shi an ga zai iya tafiya a cikin ƙungiya. Sannan kuma za mu yi aiki da ‘yan Kannywood, musamman furodusoshi kai-tsaye, saboda su ne su ke yin finafinai yadda in sun yi fim za su kawo mana su biya mu mu fassara.
“Kuma ɗaya daga cikin abubuwan da su ke ci mana tuwo a ƙwarya shi ne ana bayar da aikin a ƙurarren lokaci, don sai a bayar da fim a ce a fassara shi cikin kwana ɗaya ko biyu; ka ga dole ba za a samar da abin da ake so ba.
“Ya kamata a ce an bai wa mutum wata ɗaya wajen fassara, don shi ne zai sa a samu fassara mai kyau. Don haka wannan ƙungiya za ta kankaro wa masu fassara darajar su kuma ya zamana ana biyan su haƙƙin su yadda ya kamata.
“Kuma a hukumance muna samun goyon baya na cewa idan ka yi fim ka kai, to ba za a karɓa ba in dai ba a wannan ƙungiyar aka fassara shi ba.
“Amma fa kafin a je ga wannan ɗin sai an wayar wa da mutane kai, musamman su furodusoshi da daraktoci, musamman da yake a yanzu an zo wani zamani na Netflix ɗin nan wadda idan ka yi fassara da ba ta dace ba, to ba za su karɓa ba duk kyan aikin.
“Don haka mun zo a daidai lokacin da ya dace kenan a lokacin da Netflix ta shigo Kannywood don haka ‘yan wannan ƙungiyar mu na fatan za mu samu aikin yi.
“Kuma daga yanzu zuwa watan Yuni mu ke fatan samar da duk wani tsari na gudanar da harkar ƙungiyar.”
Ƙungiyar da ta na karkashin jagorancin Kabiru Musa Jammaje a matsayin shugaban riƙo, sai Ummalkhari wadda ta yi fassarar fim ɗin ‘Mansoor’ a matsayin mataimakiya, sai Huzaifa Sani Iliyasu a matsayin Sakatare.