• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Tuesday, June 17, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Darakta Amir Mairose ya rikiɗa jarumi tare da kiran ‘yan fim su rama wa kura aniyar ta

by DAGA MUKHTAR YAKUBU
December 19, 2022
in Labarai
0
Amir Mairose (Garzali na cikin 'Daɗin Kowa')

Amir Mairose (Garzali na cikin 'Daɗin Kowa')

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

DARAKTA Amir Mairose, wanda ya daɗe ana damawa da shi a Kannywood, ya yi kira ga ‘yan fim da su taimaka su riƙa sanya shi a finafinan su kamar yadda ya riƙa yi masu a baya.

Mairose dai ya rikiɗe ne ya koma jarumi a cikin shirin nan mai farin jini na ‘Daɗin Kowa’ da ake nunawa a Arewa24 inda ya ke fitowa a matsayin wani ɗan daba mai suna Garzali.

A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da shi, sabon jarumin ya ce, “Kamar dai yadda aka san ni ina yin daraktin tun wajen shekaru ashirin, wato tun daga fim ɗin ‘Jarin Ibro’, sannan kuma ni furodusa ne tsawon wannan lokacin, to har kullum ita rayuwa al’amuran su na canzawa. Wannan ya sa na ga a yanzu ni ma lokaci ne da ya kamata a ce na canza ɗin, kuma na gano su jarumai su na da wata  alfarma idan sun je wani waje.”

Amir Mairose a Nijar

Ya ci gaba da cewa, “Hakan ce ta sa na rubuta labaran da na ke ganin zan hau su a matsayin jarumi. To amma dai ban samu yi ba sai kawai na samu kai na a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ a matsayin jarumin duk da cewa farkon lokacin da zan fara sai da ƙwalla ta zo mini, na ga a baya ni na ke sawa a yi, kuma a yanzu na dawo ni zan tsaya a ba ni umarnin abin da zan yi, kuma aka ɗauko wani rol na daba da ban san shi ba aka ba ni, amma dai na koma na sabar wa kai na yanayin ɗan daba mai shaye-shaye, kuma alhamdu lillah na yi abin da ake so a gani a fim ɗin. 

“Kuma daga nan duniya ta ɗauka, duk inda na je ana kiran sunan Garzali, har ta kai a yanzu na samu karɓuwar da ban taɓa tunanin ta ba. Don ko da na je Nijar a kwanakin baya sai da aka ɓoye ni! Kuma daga nan na gano shi fim alfarma ce a duniya.”

Amir ya bayyana farin ciki da samun wannan damar da ya yi. Ya ce a yanzu har an fara kiran sa zuwa wasu finafinan.

“Ina fatan ‘yan fim da na taimaka wa a baya a yanzu za su rama wa kura aniyar ta,” inji shi.

Haka kuma Amir Mairose ya yi godiya ga mutanen da su ka karɓe shi a matsayin jarumi, tare da fatan za su ci gaba da kula da shi idan za a yi fim kamar yadda ya riƙa yi wa sauran jarumai a baya.

Loading

Tags: Amir MairoseArewa24Daɗin Kowaɗan dabafurodusaGarzaliJarin Ibrojarumi
Previous Post

Nunu, ‘yar jaruman Kannywood Samira Ahmad da TY Shaban, ta cika shekara 9

Next Post

Jarumin Kannywood Hannafi Rabilu Musa Ɗan Ibro ya ci gasar mota

Related Posts

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry
Labarai

Furodusan Kannywood, Abubakar Galadima ya zama jakaden garin sinadarin girki na Zahir Spice Curry

June 15, 2025
Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
Next Post
Hannafi Rabilu Musa Ɗan Ibro ya na karɓar makullin motar da ya ci a gasar

Jarumin Kannywood Hannafi Rabilu Musa Ɗan Ibro ya ci gasar mota

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!