DARAKTA a Kannywood, Kamal S. Alƙali, ya yi hamdala kan matar da ya aura, wato amaryar sa, Hauwa S. Garba, wadda su samun ƙaruwar ɗa namiji da ita kwanan nan.
A ranar 23 ga Disamba, 2023 ne Hauwa, wadda tsohuwar jarumar Kannywood ce, ta haihu a wani asibiti mai zaman kan sa a cikin garin Kano.
Kamal ya raɗa wa jaririn nasu suna Ahmad.

Cikin murna da jin daɗi, lokacin da mujallar Fim ta nemi jin ta bakin fitaccen daraktan kan haihuwar, sai ya ce, “Ina godiya ga Allah da ya nuna mini wannan lokaci da mata ta, Hauwa S. Garba, ta yi bayan wata 10 da auren mu. Domin kuwa an ɗaura mana aure ne a watan Maris ɗin da ya gabata, wanda a cikin wata na 10 Allah ya azurta mu da samun wannan ƙaruwa.

“Ina godiya ga Allah da ya sa na samu mata ta kirki wadda duk wani abu na burin rayuwa bai dame ta ba.
“Saboda in ka kula da irin kallon da ake yi wa ‘yan fim, musamman mata, a kan zamantakewar aure, ni sai na ce alhamdu lillah. Don mu na zama lafiya da juna da kuma fahimtar juna.
“Ina fatan Allah ya ƙara mana zaman lafiya a tsakanin mu da ita da uwargida, ya zama mu na zaman lafiya cikin aminci.”
To amin ya Allah, darakta.
