A JIYA Lahadi, 20 ga Maris, 2022 aka gudanar da gagarumin bikin auren mawaƙi Albashir Hamza Yareema da kyakkyawar amaryar sa, Sadiya Abdullahi Ahmad.
Idan kun tuna, mun ba ku labarin ɗaurin auren su da aka yi a ranar Juma’a da ta gabata, 18 ga Maris, 2022 a Kaduna a kan sadaki N100,000.
A labarin, mun sanar da ku cewa an ɗaga ranar dinar auren zuwa Lahadi domin a samu halartar membobin ƙungiyar ‘Yahaya Bello Network Group’ (YBN) wadda shi angon jakaden ta ne.
Da farko dai an saka cewa za a fara shagalin bikin da misalin ƙarfe 8:00 na dare. Hakan ya sa matasan ‘yan fim da mawaƙan da ke ƙungiyar YBN reshen Jihar Kaduna su ka fara tururuwar zuwa bikin. Kafin ka ce kwabo ɗakin taron da ke otal ɗin NUT ya cika maƙil, duk inda ka juya hulunan YBN za ka gani a kan maza da mata. Maza sun yi ankon shuɗiyar shadda da malum-malum, amma hula hana-sallah ce a kan su, mata kuma sun ɗinka atamfa.

Ango Albashir, wanda abokan sa ke kira Jakada a yanzu, sho da amarya ba su shigo ɗakin taro ba sai misalin ƙarfe 9:10 na dare. Shigowar su ke da wuya, aka fara abin da ya tara jama’a.
Bayan Abdullahi Abbas (Ubangari) ya gabatar da jawabin maraba, sai aka kira amarya da ango, inda aka saka masu waƙar da shi angon ya yi wa Abdullahi Abbas ɗin, wanda da ma shi ne shugaban su na YBN reshen Jihar Kaduna.
An yi ɓarin naira a wannan lokaci. Amma kuma sai uban gayyar ya shigo, wato Abdul Amart Mohammed, sannan aka fara biki. Ya shigo ɗakin taron da misalin ƙarfe 9:40 na dare tare da wasu daga cikin tawagar sa.
A daidai wannan lokacin sai aka saka waƙar da Albashir ya yi wa Amart. Nan da nan kuwa wurin ya cika da jama’ar YBN da kuma jagoran su, inda aka yi ta ruwan naira kamar yadda aka saba a wurin bikin ‘yan fim.
Biki dai ya yi biki, domin an ci an sha, an kuma gyatse.

Wani abin mamaki da wakilin mujallar Fim ya hango shi ne halartar budurwar angon a wurin dinar, wato Ummi Hutu, duk da cewa ba ita ya aura ba.
Duk wanda ya san Albashir, ya san soyayyar sa da jarumar, haka ita ma duk wanda ya san ta ya san soyayyar ta da Albashir. Amma kuma sai Allah ya sa ba ita ya aura ba duk da irin tsananin ƙaunar da su ka yi wa juna.
Hasali ma dai, da ana saura mako biyu katin gayyatar ɗaurin auren Albashir da Sadiya ya bayyana a industiri, sai ce-ce-ku-ce da ƙananan maganganu su ka bazu a masana’antar Kannywood ta Kaduna, inda wasu ke cewa Albashir bai kyauta wa Ummi ba, wasu kuma na cewa Allah ya yi ba matar sa ba ce.
Sai Ummi ta burge mutane da dama, domin kuwa ta ɗauki ƙaddara da kuma haƙuri, wanda ya sa ba ta guje shi ba. Hasali ma yawancin shirye-shiryen bikin da ita aka yi. Haka kuma ita ta fitar da ankon da mata su ka saka a wurin dina.
Albashir dai Bafulatani ne, haka ita ma amaryar tasa, kuma auren zumunci su ka yi, domin ‘yar’uwar sa ce.

Wasu daga cikin waɗanda su ka halarci wannan dina dai sun haɗa da Abdul Amart, Sadiq Mafia, Tahir I. Tahir, Nura Manaja, Abdullahi Abbas, Jamil Nafseen, Ɗanladiyo Mai Atamfa, Abdullahi Abu Uku, Abban Waƙa, Muhammad Show Man, Ibrahim Saminaka, Maikano Bagobiri, Madam Korede, Hafsat Jos, Amina Buzuwa, Raliya Muhammad, Jamila Lasco, Fati K/Mashi, Zee Shewa da sauran su.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba, amin.





