FITACCEN furodusa a masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Mustapha Ahmad, wanda aka fi sani da Alhaji Sheshe, ya musanta zargin da darakta Sunusi Oscar442 ya yi na cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta tilasta maye sunan sa da na wani daraktan a wani fim saboda saɓanin da ke tsakanin sa da shugaban hukumar.
Idan kun tuna, a ranar Litinin da ta gabata, 25 ga Yuli, 2021, mujallar Fim ta wallafa hirar ta ta farko da Oscar442 inda ya zargi shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), da ɗaukar wasu matakai na musguna masa saboda bambancin siyasa da ke tsakanin su.
Oscar442 ɗan jam’iyyar PDP ne, yayin da Afakallah ya ke aiki a gwamnatin da APC ta kafa.
Oscar442 ya faɗa wa mujallar Fim cewa: “Ina da matsala da shugaban Hukumar Tace Finafinai. Ba ya ƙauna ta gaba ɗaya, don haka ba wani abu da zan iya yi don in rayu a masana’antar Kannywood in dai ya na nan. Sau da yawa zan yi fim, zai ce in dai ni ne ba zai duba fim ɗin ba. A satin nan ma akwai wani fim ɗi na da na yi, na kamfanin Sheshe, ya ce a cire suna na, in dai ni ne fim ɗin ba zai fita a cikin Jihar Kano ba. To mai kamfanin ya sa aka kira ni, ya ce ga abin da Hukumar Tace Finafinai ta gaya masa. Na ce masa ya yi haƙuri a cire, ba wani abu ba ne ba. Haka aka cire, aka maye suna na da na Ali Gumzak a cikin wannan fim ɗin.”
To amma shi a nasa ɓangaren, Alhaji Sheshe cewa ya yi rashin bin doka ne ya sa aka cire sunan daraktan tun kafin su kai wa hukuma fim ɗin domin tacewa, ba wai Afakallah ne ya sa aka cire sunan ba.
A zantawar sa da mujallar Fim a ofishin sa da ke Kano, Alhaji Sheshe ya kawo wasu dalilai waɗanda ya ce su ne su ka jawo aka cire sunan daraktan daga cikin fim ɗin mai suna ‘Juwairiyya’, wanda aka ɗauka tsawon lokaci kafin ya fito.
Ya ce, “Na wayi gari da ganin labari a kan cewa Hukumar Tace Finafinai ta cire sunan darakta Sunusi Oscar442 kan cewar in dai da sunan sa to ba za ta duba fim ɗi na ba. To, maganar gaskiya Hukumar Tace Finafinai ba ita ce ta sa na cire Oscar daga fim ɗin ‘Juwairiyya’ ba.
“Abin da ya faru shi ne fim ɗin ya kai kusan shekara uku da ɗauka kafin Hukumar Tace Finafinai ta sa dokar cewa duk wani ɗan fim a Kano sai ya yi rijista da ita. A lokacin mu ka ɗauki fim ɗin sai kuma aka samu tsaiko wajen fitowar sa tun a lokacin kafin a sa dokar kenan, sai kuma yanzu mu ke so mu saki fim ɗin.
“Duba da tsarin Hukumar Tace Finafinai na duk fim ɗin da a yanzu idan akwai wani wanda ba shi da rijista da ita ba za ta duba ba, shi ne ya sa mu ka ɗauki gaɓarar sanar da duk wanda ya san ba shi da rijista a cikin mutanen da mu ka ɗauki fim ɗin da su da su yi haƙuri za mu cire sunan su za mu sa na waɗanda su ke da rijista.”
Ya ƙara da cewa, “Mu na so za mu fitar da fim ɗin mu a kasuwa, yanzu kuma ga shi akwai sunan sa a ciki kuma ba shi da rijista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano. Hakan ya sa na sa aboki na, Sani Kandi, ya kira wo Sunusi Oscar a waya su ka yi magana ta fahimtar juna, ya kuma gane cewa matsalar daga gare shi ne na rashin yin rijista da hukuma.
“Lokacin da abin ya faru, na ba shi shawarar ya je ya yi rijista tun lokacin da aka fara yin rijista ta farko. Na ce masa shi darakta ne, ya kamata ya zo ya yi rijista saboda a ci gaba da sana’a tare.

“Sai ya nuna min shi ba zai yi rijista ba wani mutum ya sa shi a aljihu, shi harkokin sa ya fi yi a Abuja, wato waƙe-waƙe ne, don haka ba shi da buƙatar yin rijista a Jihar Kano daga nan zuwa shekara biyu ko uku ma nan gaba.
“To, duba da haka ya sa na nemi izinin sa kan cewa na cire sunan sa saboda zan kai fim ɗi na a duba min don ina so na saki fim ɗin a kasuwa. A nan ya amince, ya mana fatan alkairi. Na cire sunan sa.”
Alhaji Sheshe ya ce, “Ana cikin wannan abu, kwatsam! sai na ga ya yi hira a kan cewa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta ce ba za ta duba fim ɗin ba in dai da sunan sa a ciki. Ni kuma ba mu yi haka da Hukumar Tace Finafinai ba.
“Kai, hasali ma ba ta san waye daraktan fim ɗi na ba, kawai dai na san cewa idan na kai fim ɗi na da sunan daraktan da ba shi da rijista da hukumar, to ba za ta duba ba.
“Ina tabbatar da cewa shi kan sa fim ɗin ba a kai shi wurin Hukumar Tace Finafinai da sunan sa ba, ballantana su ce ba za su duba ba.
“Kuma mun yi finafinai guda biyu da Oscar, ɗaya mai suna ‘Ƙazamin Shiri’ da kuma wannan ‘Juwairiyya’, wanda a lokacin da ‘Ƙazamin Shiri’ ya fita babu doka ta cewar sai ka na da rijista kuma na kai hukuma ta duba fim ɗin.
“Kuma a lokacin ya na jam’iyyar PDP, kuma da man shi bai taɓa fita daga ita ba, ni ma kuma ɗan PDP ne, mu na ma da ‘yar tsama tsakanin mu da APC a lokacin, amma na kai fim ɗin aka duba min aka ban shaida wato satifiket, na haska shi a sinima. Yanzu ga shi ana sa shi ma a tashar Arewa24.”
Alhaji Sheshe ya jaddada cewa babu wata alaƙar siyasa da ta sa aka cire sunan Oscar442 daga wannan fim ɗin domin kuwa ya ce idan da alaƙar siyasa ce, to da shi ma an cire sunan sa don shi ma ɗan PDP ne, kowa ya sani, kuma duk abin da wani mutum ya ke ji ya ba wa PDP gudunmawa da rayuwar sa ko da jikin sa shi ma ya ce ya bayar in dai a masana’antar fim ne.
“Irin gudunmawar da mu ka ba wa PDP ba lallai wasu daga cikin masu tafiyar PDP sun bayar ba,” inji shi.
Babban furodusan ya yi kira ga abokan sana’ar sa da su yi ƙoƙari su riƙa bin dokar gwamnati domin a cewar sa ita gwamnati ba a ja da ita, ikon Allah ce.
Ya ce: “Ka bi dokar ta ka zauna lafiya, ka ƙi bin dokar ta ka shiga ruɗani. Wannan kira ne ga abokai na na sana’a da kuma na cikin jam’iyya ta ta PDP da su ke harkar fim.”
