A DAIDAI lokacin da ake murnar shiga sabuwar shekara, shi kuma editan finafinai a Kannywood, Yakubu Hafizu Ɗandago, wanda aka fi sani da Malam Alhaji Edita, angwancewa ya yi da sahibar sa, Safiyya Sa’eed Mika’iku.
A ranar Lahadi, 1 ga Janairu, 2023 aka ɗaura auren su a Masallacin D.O. da ke Gwale a cikin Birnin Kano da misalin 11 na safe.
‘Yan fim da dama sun halarci ɗaurin auren.

Tun kafin ranar ɗaurin auren an yi shagalin biki a ranar Asabar a Hazeen Events Centre da ke Farm Centre.
Allah ya ba da zaman lafiya da fahimtar juna.