FITACCIYAR jaruma Farida Jalal ta bayyana cewa hukuncin da ƙungiyar ƙwararru masu shirya finafinan Hausa ta ƙasa (MOPPAN) ta yanke na korar Rahama Sadau sam bai dace ba.
Farida, wadda tsohuwar jaruma ce a Kannywood, ta bayyana hakan ne yayin da ta ke nuna alhinin ta a ranar Litinin.
Ta tunatar da cewa ba wannan ba ne karon farko da aka kori Rahama daga industiri, kuma ta tabbatar za a sake dawo da ita komai daren daɗewa.
Ta ƙara da cewa kamata ya yi shugabannin ƙungiyar su samar da hanyoyi da za su dinga ladabtar da duk wani ɗan fim da ya aikata laifi irin na Rahama Sadau, amma ba kora ba.
Farida ta ce al’umma ba za ta daina kallon Rahama a matsayin jarumar Kannywood ba, kuma ko da ta sake aikata wani laifin za a ci gaba da alaƙanta ta ne da masana’antar.
“A da an kore ta, kuma an dawo da ita, yanzun ma wannan kora ba za ta yi aiki ba,” inji ta.
Jarumar ta bada shawarar cewa kamata ya yi jaruman Kannywood su haɗe kan su tare da ciyar da masana’antar gaba, ba wai su riƙa jifan juna da munanan kalamai ba.
Ta ce, “Abin takaici ne yadda wasu daga cikin mu su ka dinga aibanta jarumar da yin tsinuwa gare ta bayan kuma kowannen mu mai laifi ne.”
Ta nuna nadamar ta da cewa, “Ya kamata a ce mun yafe mata. Mu na yi wa Allah laifi kuma ya na yafe mana matuƙar mu ka nemi gafarar sa.”
Farida ta ce ko me ya faru Rahama Sadau ce ta jawo wa kan ta amma tunda ta tuba kamata ya yi a yafe mata.
Ta kuma yi kira ga jaruman masana’antar da su haɗe kan su tare da yin amfani da koyarwar addinin Musulunci a dukkan al’amuran su na yau da kullum.