• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Monday, June 16, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Fati KK ta koma wa tsohon mijin ta

by DAGA ABBA MUHAMMAD
February 13, 2021
in Ranar Murna
5
Fati KK ta koma wa tsohon mijin ta
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

FITACCIYAR jarumar finafinan Hausa, Fatima Mohammed Sadisu KK, wadda aka fi sani da sunan Fati KK, ta sake yin aure bayan shekara uku ta na zawarci. 


Sai dai a wannan karon ba wani sabon mutum ta aura ba, ta koma gidan tsohon mijin ta ne, Alhaji Mu’azu Yusuf, wanda lauya ne a Kano. 


An ɗaura auren a jiya Juma’a, 12 ga Fabrairu, 2021 a gidan su amaryar da ke Sabon Kawo, Kaduna.


Mu’azu dai shi ne mijin ta na biyu, kuma su na da ‘ya’ya biyu, Ahmad da Yasmin.


A auren ta na farko, wanda ta yi a Birnin Kebbi bayan an ɗaura shi a ranar 1 ga Nuwamba, 2014, ta haifi ‘yar ta ta fari, wato Hafsat, wadda ake wa laƙabi da Preety.

Mujallar Fim ta fahimci cewar Fati KK ta saba ɓoye duk wani aure da aka ɗaura mata, sai dai daga baya a ji labari. Haka ta yi a auren ta na farko da na biyu.


A lokacin waɗancan aurarrakin, yawancin mutane sun samu labarin ne ta wata hanya, amma wakilan mujallar Fim sun samu halartar ɗaurin aure, wanda daga baya mun buga cikakkun bayanai. 


A wannan karon, sai dai kawai gani aka yi jiya da yamma jarumar ta Kannywood ta ɗora wasu hotuna inda ta yi shigar amarya kamar a wurin taron bikin nata. 


Haka kuma ta rubuta kalaman godiya ga Allah, ta ce: “Alhamdu lillah, Alhamdu lillah,  Alhamdu lillah, Alhamdu lillah, Alhamdu lillah… Allah ka ba mu zaman lafiya ni da miji na. Ya Allah ka sa mutuwa ce za ta raba mu.”


Sai dai kuma ba ta faɗi wanda aka ɗaura auren nata da shi ba, illa dai ta kira kan ta da “Mrs M.”, wanda hakan dai na nufin “matar Mu’azu” kamar yadda wannan mujallar ta gano.

Wata majiya ta tabbatar wa da mujallar Fim cewa har Fati ta tare a gidan mijin ta a Kano.

Amarya Fati KK  wajen walimar sabon auren ta da aka ɗaura jiya
Amarya Fati KK wajen walimar sabon auren ta da aka ɗaura jiya


Wakilin mu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin tsohuwar jarumar, amma hakan bai yiwu ba domin a duk lokacin da ya kira ta sai ta danna ƙin amsa kiran nasa a waya. 


Wakilin namu ya so ya samu ƙarin bayani game da auren daga gare ta da kuma makomar shagon sayar da kayan amfani a cikin gida da ta buɗe kwanan baya a Kaduna.

Fati da Mu’azu a wani tsohon hoto nasu


Idan masu karatu za su iya tunawa, a lokacin da auren ta da Alhaji Mu’azu ya mutu a cikin 2018, tsohuwar jarumar ta faɗa wa mujallar Fim a wata hira da mu ka buga cewa dangin sa ne su ka kafa mata ƙahon zuƙa da damuwa kala-kala, har su na yi mata gori.


Shi ma Mu’azu, a wancan lokacin ya faɗa wa mujallar Fim cewa Fatin ce ta bijire masa saboda zai yi mata kishiya.

Amma a hirar ta da Fim a lokacin, Fati KK ta ƙaryata zargin da dangin nasa da shi su ka yi mata, ta ce don me za ta hana shi ƙara aure bayan lokacin da ya aure ta ɗin ita ma ta samu uwargidan sa tare da shi? Ta ce ya faɗi haka ne domin ya ɓata mata suna a idon duniya.


To, yanzu dai komai ya wuce, sun sasanta kan su.


‘Yan fim da dama sun taya Fati murnar wannan aure da ta sake yi.


Mu ma mu na addu’ar Allah ya ba su zaman lafiya, ya kasance mutu-ka-raba.

Amarya Fati KK tare da tsohuwar jaruma Wasila Isma’il a wajen bikin
Amarya Fati da ango Mu’azu a ranar maida auren su
Previous Post

Shugaban jaridun Manhaja da Blueprint ya sabunta rajistar sa a APC

Next Post

Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Related Posts

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu
Ranar Murna

An ɗaura auren darakta a Kannywood, Al-Amin Ciroma da ‘yar’uwar sa Sharifatu

May 2, 2025
Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu
Ranar Murna

Ƙarshen tika-tika, tik! A’ishatulhumaira ta zama matar Rarara ta huɗu

April 25, 2025
Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 
Ranar Murna

Darakta Al-Amin Ciroma zai yi amarya a watan gobe, shekaru biyu bayan mutuwar auren sa da Wasila Isma’il 

April 20, 2025
Ahlan tare da 'yar sa Hassana, amaryar mako mai zuwa
Ranar Murna

Jarumi a Kannywood, Ahlan zai aurar da ‘yar sa Hassana

February 16, 2025
Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir
Ranar Murna

Daɗi kan daɗi: Marubuciya Bilkisu Yusuf Ali ta samu jika da digirin digirgir

December 20, 2024
Next Post
Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Mutanen Neja sun yi murna da shirin tallafin Gwamnatin Tarayya ga matan karkara

Comments 5

  1. Yusuf Ubale says:
    4 years ago

    Allah Ya basu zaman lafiya

  2. Sunus says:
    4 years ago

    GASKIYA NA TAUSAYAMATA LOKACIN DA AMRANTANTA DINNAN YA MUTU,HAR TAKE CEWA YAZA AYI ACE MUTUM YAYI AUREN DAZAIFITO HARKUMA YABUDE MAHAIFA YAITA HAIHUWA???
    ITA TAYI AMRENE MUTU KARABA SAIKUMA YAN’UWANSA SUKA TUSOTA A GABA SUKA KAFAMATA KAHON ZUKA 😥

  3. Abdullahi Leader says:
    4 years ago

    Alhamdulillah….
    Ina taya jarumata murnar, amarcewa..
    Allah ya bada zaman lafiya da Alkhairi…

  4. Muntariamirudoguru says:
    4 years ago

    Masha Allah

  5. Esther says:
    3 years ago

    Allah ya zaunar da ku lafiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!