A YAU Lahadi, 21 ga Janairu, 2024 aka ɗaura auren ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayi Malam Aminu Muhammad, wanda aka fi sani da Aminu Mai Chemist, kuma Alhaji Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ na tashar Arewa 24.
An ɗaura auren Fatima Aminu Muhammad (Alishba) da abin ƙaunar ta Muhammad Sani Muhammad da misalin ƙarfe 10:00 na safe a masallacin Abdurrahman Bin Auf da ke kusa da gidan su a Haye, Hotoro North, Ring Road – Eastern Bypass, Ƙaramar Hukumar Nassarawa, Jihar Kano, a bisa sadaki N100,000.

An ɗaura auren Fatima ne a daidai lokacin da mahaifin ta ke cika wata tara da kwana 13 da komawa ga Mahaliccin sa.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a tagari, ya sa mutu-ka-raba.
Allah kuma ya jiƙan Malam Aminu AZ da rahamar sa, ya sa Aljanna makoma.