FURODUSA a Kannywood, Honarabul Abdullahi Abubakar, wanda aka fi sani da Abdullahi Jiya Da Yau, ya yi bankwana da gwauranci.
An ɗaura auren shi da santaleliyar masoyiyar sa, A’isha Adam (Ashnah), a yau Asabar, 1 ga Fabrairu, 2025 da misalin ƙarfe 2:00 na rana, a Titin Nagoggo da ke Kwanar Chanchangi, Tudun Wada, Kaduna, a kan sadaki N200,000.

Kasancewar Abdullahi shi ne Kansilan unguwar Maiburji a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa, ɗaurin auren ya samu halartar manyan ‘yan siyasa da kuma sauran abokan aikin sa kansiloli su goma sha ɗaya.
Haka kuma tsohon ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Malam Sama’ila Sulaiman, shi ne wanda ya wakilci Abdullahi, ya karɓar masa auren.

‘Yan siyasa da suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Honarabul Tukur Musa (TK), Ahmad Isma’il, Yusuf Waza-Waza da sauran su.
Allah ya ba su zaman lafiya da zuri’a ɗayyiba.