SHUGABAN Kwamitin Dattawa na Masana’antar Kannywood, Malam Shu’aibu Yawale, ya aurar da ‘ya’yan sa guda biyu, Aminu Shu’aibu Yawale da Khadija Shu’aibu Yawale.
An ɗaura aurarrakin a ranar Asabar a masallacin Juma’a na Badar da ke Unguwa Uku Layin Yarabawa, Kano.
An ɗaura auren Aminu da Zulaihat Sadisu Ilyasu, ita kuma Khadija aka daura mata aure da Saifullahi Bilyaminu Balarabe.
‘Yan’uwa da abokan arziki daga cikin Kannywood da wajen ta sun halarci daurin auren.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa Malam Shu’aibu Yawale jarumi ne kuma furodusa. Yana daya daga cikin ‘yan fim da suka shirya fim din ‘Turmin Danya’, wanda ya kasance shi ne na farko a cikin finafinan bidiyo da aka fara yi a Kannywood.
A saƙon da ya bayyana mana bayan daurin auren, Malam Shu’aibu ya yi godiya tare da nuna jin daɗin sa ga dukkan masoya, ‘yan’uwa da abokan arziki, da suka halarci wajen ɗaurin auren, da ma waɗanda ba su samu damar zuwa ba suka aika da saƙon addu’a da fatan alheri.
Ya yi addu’ar Allah ya sa kowa ya koma gida lafiya.