Furodusa kuma jaruma a Kannywood, Amina Adamu Yusuf, ita ma ta bi sahun matan Kannywood masu hada harkar fim da kasuwanci, domin kuwa a ranar Asabar aka yi gagarumin bikin bude shagon ta da ke Titin Sheikh Muhammad Nasiru Kabara, daura da Gidan Dan’asabe, a Kano.
Taron da aka shirya shi tun daga karfe 3 na yamma, ya samu halartar dimbin manyan jarumai da ake damawa da su a Kannywood yanzu.
Bayan halartar manyan baki bisa jagorancin ogan ta a industiri, wato Abdul Amart, an yi wakokin nishadantar da mahalarta taron wadanda wasu jarumai suka yi tare da raye-raye.
Sai kuma Abdul Amart ya jagoranci bude shagon tare da yanka igiyar, bisa taimakawar ita Amina da sauran manyan jarumai.



Amina dai jaruma ce kuma ita ce furodusar fim din ‘Da Na Sani,’ sannan kuma ita ce Manajar kamfanin Abnur Entertainment na Abdul Amart.
Da take jawabin godiya bayan kammala taron, Amina ta yi godiya ga dukkan jama’ar da suka halarci taron, musamman ma dai maigidan ta, Abdul Amart, da su Bashir Maishadda, Sadiq Sani Sadiq, Ali Nuhu, Aminu Saira, Ado Gwanja, Nazifi Asnanic, da sauran su.

