UMAR UK, ɗaya daga cikin manyan furodusoshin Kannywood, ya maka fitacciyar jaruma Hafsat Idris (Ɓarauniya) a kotu, ya na neman diyya kan ƙin zuwa ɗaukar wani shirin sa na talbijin da ta yi bayan ya biya kuɗi har naira miliyan ɗaya da dubu ɗari uku (N1,300,000).
Umar, mai kamfanin UK Entertainment, ya na neman diyyar naira miliyan 10 daga jarumar a bisa tuhumar karya yarjejeniya.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa furodusan ya shigar da ƙarar ne Babbar Kotun Kano ta 14 da ke yankin Ƙaramar Hukumar Ungogo cikin birnin Kano.
A cikin takardar ƙarar da wakilin mu ya gani, Umar ya yi iƙirarin cewa ya biya Hafsat kuɗin ne domin ta fito masa a wani shirin takbijin mai suna ‘Girke-Girken Afrika’ da ya ke shiryawa. An fara ɗaukar shirin da ita, amma kwatsam sai ta yi ƙemadagas ta daina zuwa.
A cewar sa, hakan da ta yi ya saɓa wa alƙawarin da su ka yi a rubuce.
Umar ya faɗa wa kotun, a ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Abdullah, cewa ya samu asara mai yawa sakamakon daina zuwa shirin da Hafsat ta yi.
Saboda haka ya buƙaci kotun da ta umarce ta ta biya shi diyyar naira miliyan 10, kuma ta dawo masa da shigar cinikin da ya ba ta.
A ranar da aka zauna a kotun dai Hafsat ba ta je ba, amma ta shigar da tata kariyar a rubuce a kotun ta hanyar lauyan ta.
Daga nan alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 19 ga Oktoba, 2021.
Alƙali Ibrahim ya bada umarnin a sake kai wa jarumar sammaci domin ta halarci kotun a ranar da za a koma.
Mujallar Fim ta samu labarin cewa Umar UK ya yi yarjejeniya da wani gidan talbijin ɗin satalayit da ke ƙasar Ghana mai suna ‘Gaskiya TV’ ne domin su riƙa nuna shirin girke-girken, kamar yadda tashar talbijin ta ‘African Magic’ ke haska shirin “Girke-Girken Hauwa Maina”.
Sakamakon rugujewar harkar kasuwancin finafinan Kannywood, furodusoshi da dama sun faɗaɗa tunanin su wajen shirya wasu shirye-shirye da za a kalla, musamman ta hanyar talbijin, sinima ko YouTube.
Binciken mujallar Fim ya nuna cewa tun da fari, naira miliyan biyu Hafsat ta buƙaci Umar ya biya ta, amma bayan roƙon ta da ya yi sai ta yi masa ragin ɗari bakwai.
A yarjejeniyar aikin, an amince cewar idan za a fita aikin za a sanar da ita a kan lokaci, sannan idan ta na da uziri za a iya ɗagawa.
A cewar majiyar mu, an yi nisa da aikin, rannan sai aka sanar da jarumar cewa gobe za a fita zuwa aikin, amma ita kuma ta na Kaduna, don haka ta buƙaci a ɗaga ranar.
“To da yake sau biyu kenan ana ɗagawa, sai Umar ya ji haushi, ya ƙi ɗaga ranar. Sai ya maye gurbin Hafsat da Jamila Nagudu, kuma ya cire Hafsat daga shirin,” inji mai ba mu labarin.
Sakamakon haka rai a ɓaci a ɓangarorin biyu, inda a ƙarshe Umar ya nemi jarumar da ta dawo masa da kuɗin sa.
Majiyar mu ta ce ganin halin da ake ciki sai fitaccen furodusan nan, Tahir Elkinana, ya kira Umar da Hafsat taron sasantawa a ofishin sa.
Da aka zo taron, sai Umar ya zo da takardar ƙarar Hafsat, ya miƙa wa Elkinana, wanda jami’in gwamnatin jihar ne. “Haka kuma a daren sai ya saka labarin a gidan rediyo, aka yayata,” inji majiyar mu.
Yaɗa labarin a rediyo ya ɓata wa Hafsat rai, har ta yi niyyar za ta kai Umar kotu a kan ya ɓata mata suna idan an gama shari’ar su.
Da ranar zuwa kotu ta zo, aka fara sauraren ƙarar.