ƊAYA daga cikin dattawan Kannywood kuma tsohon shugaban Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Sa’idu Isah Gwanja, ya nuna ɓacin rai kan yayata tallafin azumi da fitaccen mawaƙi Alhaji Dauda Abdullahi Kahutu (Rarara) ya yi masa kwanan nan.
A ganin sa, yayata kyautar tamkar riya ce, kuma cin zarafi ne a gare shi da sauran ‘yan masana’antar.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta ba ku labari a shekaranjiya Juma’a cewa Rarara ya raba kyautar naira dubu hamsin-hamsin ko talatin-talatin ga wasu ‘yan fim na da da na yanzu a matsayin tallafin azumin watan Ramadan da ke ƙarewa a yau.
Da ma can akwai masu ƙorafi a bayan fage cewa yadda Rarara ya ke yayata kyautar kuɗi ko mota da ya ke raba wa ‘yan Kannywood, musamnan a soshiyal midiya, riya ce, amma su na karɓa saboda yanayin rayuwar a yau.
Babu wanda ya taɓa fitowa fili ya soki lamirin Rarara kan al’amarin sai yanzu.
A zantawar da ya yi da mujallar Fim a ofishin sa da ke Titin Zariya a Kano, Sa’idu Gwanja, wanda yayan fitaccen mawaƙi kuma jarumi Ado Isah Gwanja ne, ya yi cikakken bayani kamar haka: “To ni a matsayi na na Sa’idu Isah Gwanja wanda ya ke tsohon shuga ne a masana’antar kuma a yanzu ina cikin Gidauniyar Kannywood wanda kuma zan iya cewar da ire-iren mu ne masana’antar ta samu gindin zama, amma a yanzu ina magana ne a matsayin kai na, ba ina wakiltar kowa ba, zan iya cewa wannan shi ne karo na biyu da aka kira ni domin karɓar kyauta daga wajen Rarara.
“Na farko an yi a wancan azumin da ya wuce. Don ba zan manta ba, akwai aboki na, Hafizu Bello, ya kawo mini dubu hamsin ya ce daga wajen Rarara. To daga baya sai na ji ana ta kira na ana cewa ana ta yayatawa a midiya ana cewa ina cikin waɗanda aka bai wa tallafin dubu hamsin.
“To, gaskiya har ga Allah a lokacin na yi ƙoƙarin na mayar da ita, sai waɗanda mu ke tare da su su ka hana ni. Kuma na so na bayar da shawara ta midiya tunda su ma ta nan su ka bayar, don na nuna musu cewa ba daidai ba ne. To a lokacin dai ban ce komai ba.
“To a wannan karon ma sai aka ƙara kira na, inda Hassan Giggs ya kira ni ya ke cewa akwai Aisha Humaira ta na kira na, ya ce, ‘Saƙo ne daga ofishin Rarara, ka zo ka karɓa.’ Sai na ce, ‘To na gode, Allah ya saka masa da alkhairi, amma dai ku mayar masa ku ce ba na so’.
“Saboda abin da ya sa, kyauta ko waye kai ba ka wuce a ba ka kyauta ba, domin maganar da na ke yi maka abin da aka ce na je na karɓa a halin da na ke ciki ina da buƙatar su, amma ko wanda na karɓa a shekarar da ta wuce ban yi amfani da su ba, saboda na ji ƙasƙanci ya shiga cikin zuciya ta.
“Ni Sa’idu Gwanja, wallahi ba ni da ƙara’in riƙe kuɗi kuma ba ni da ƙara’in rayuwa ta wani abu da Allah ya ke yi wa mutum, domin duk abin da Allah ya ke yi ya yi mini, ni Sa’idu Gwanja. Saboda haka, duk abin da za ka ba ni ban so idan da ƙasƙanci a ciki.
“Allah bai ƙasƙanta ni ba, to babu wani da ya isa ya ƙasƙanta ni. Domin a yanzu ‘ya’ya na 17, na 18 ya na kan hanya. Ina da marayu 3 a waje na, ka ga 21 kenan. Ga su Ado mahaifan mu sun rasu, su na hannu na. Kuma mata na 3. Na yi gida. Saboda haka duk abin da zai ƙara samu na a yanzu ba ƙara’in sa zan yi ba.
“Don haka idan shi Rarara bai san muhimmanci mu a Kannywood ba, su waɗanda su ke gindin sa ai sun san ko mu su waye. Don haka bai kamata idan za a ba mu abu, duk da ba raina abin na yi ba, to a bi ta hanyar da ta dace ta mutuntawa da mutunci.
“Yara da yawa su na yi mana kyauta, amma babu wanda ya taɓa ji. Kuma mun raini wasu, ko kallon mu ba sa yi.
“Saboda haka, idan za a gyara wannan abin to a gyara, idan kuma ba za a gyara ba, to a ci gaba da yi, rayuwa ce!”
Gwanja ya kuma miƙa saƙo kai-tsaye ga shi kan shi Rarara, inda ya ce: “Ina kuma ƙara kira ga Rarara, ban fi ƙarfin ka yi mini kyauta ba, amma ina yi maka kashedi, idan ka yi niyyar za ka yi mini kyauta, to ka san ni, ka san waya ta, ka neme ni ka ba ni. Ba girman kai ba ne. Amma kada a ƙara saka suna na a midiya a kan za a ba ni kyauta ko da sun kai miliyan 50; ko ma nawa ne, domin ba na tsoron kowa yanzu a cikin harkar fim, don a shekaru na yanzu ba na shakkar kowa, kuma ba na kwaɗayin kayan kowa, ba na tunanin wani abu da ka ke da shi zai tsone mini ido matuƙar da cin mutunci da cin zarafi.
“Don haka, ka tambayi abokai na da su ke kusa da kai da waɗanda su ke da kuɗaɗe, sam ba na bi ta kan su.
“Don haka na gode wa Allah, ni Sa’idu Gwanja. Allah ya wadatar da ni da abin da na ke samu, kuma iyali na sun yarda da rayuwar da mu ke ciki.
“Don haka ina ƙara yi maka kashedi, har yanzu idan za ka yi mini kyauta ƙofa ta a buɗe ta ke, amma dai ka yi mini ita cikin mutunci, ka yi ta ta addini da aka ce ka yi kyauta da dama hagu ba ta sani ba. Saboda na fi ƙarfin wannan. Da kai da yaran da su ka san darajar mu a baya, kuma a yanzu su ka kwaɓar da darajar, ana zuwa ana tozarta mu ana so a nuna wa mutane mu na cikin ƙaƙa-ni-ka-yi.
“Idan ko ku na ganin ko ƙane na Ado Gwanja ba ya taimako na ne, to ba haka ba ne, ya na yi mini ne ta hanyar da ta dace, ba irin wannan ba. Don haka ba na cikin siyasar harkar fim, kowa nawa ne. Wanda kuma ya ce zai rinƙa tozarta mu, to ni dai ba na so, kada a ƙara yi mini irin wannan.”
Daga ƙarshe, Gwanja ya yi gargaɗin cewa duk wanda ya ce zai yi masa kyauta irin ta Rarara, to fa za su saka ƙafar wando ɗaya da shi. Don haka idan kunne ya hi, jiki ya tsira.
A labarin da mujallar Fim ta buga, an ruwaito cewa mai taimaka wa Rarara a soshiyal midiya, Rabi’u Garba Gaya, ya lissafa rukunnai da sunayen waɗanda aka ba tallafin kamar haka:
1. IYAYE MAZA (N50,000 kowannen):
Umarun Gaya
Magaji Mijinyawa
Iliyasu Abdulmumini Tantiri
Babandi Daɗin Kowa
Bashir Bala Ciroki
Malam Haruna Hayaƙi
Malam Inuwa
Sani Idris Kauru (Moɗa)
Garba Gashuwa
Billy O
AGM Bashir
Bala Anas Babinlata
Sa’idu Gwanja
Hankaka
2. IYAYE MATA (N50,000 kowacce):
Baba Duduwa
Hajiya Tambaya
Hajiya Sadiya
Lubabatu Madaki
A’ishatu Umar Mahuta
Rabi Sufi
Ladidi Tubles
Safiya Kishiya
Hindatu Bashir
Bilkin RK
Hajiyar Nas Kaduna
Maryam CTV
Halima Kara-Da-Kiyashi
3. MATA MATASA (N50,000 kowacce):
Fati Mohammed
Ummi Nuhu
Rahama Sirace
Farida Jalal
Maryam Giɗaɗo
Hafsat Shehu
Fati Al-Amin
Rahama MK
Firdausi Kwalli
Sayyada Sadiya Haruna
4. MATAN AURE MAWAƘA (N30,000 kowacce):
A’isha Nagudu
Zainab Deman
Sa’a Vocal
Aina’u Adam Yabo
Ummi Abdullahi Yabo
Fa’iza Badawa
Maryam A. Baba
Murja Baba
Naja’atu Ta-Annabi
Firdausi ‘Yar Dubai
Asiya Sudan
Suhaima Danko
Sa’a A. Yusuf
Zuwaira Isma’il
Zahra’u Sharifai
Husaima M. Fire
Fati Rayuwa
Asma’u Sadiq