• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gargaɗin Tijjani Faraga ga masu ɓata sunan ‘yan fim: Duk wanda ya ce mana kule, za mu ce masa cas!

by DAGA ABBA MUHAMMAD
September 25, 2022
in Labarai
2
Malam Tijjani Faraga

Malam Tijjani Faraga

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

JARUMIN Kannywood, Malam Tijjani Faraga, ya bayyana cewa akwai isassun masu ilimi a masana’antar shirya finafinan, don haka duk wani wanda ya ƙara ɓata sunan ‘yan fim ba za su ƙyale shi ba.

Faraga ya yi wannan magana ne a cikin wani rubutu da ya yi ya kuma aiko wa da mujallar Fim, ya ce: “Mu na da isassun masu ilimi a masana’antar Kannywood, waɗanda duk lokacin da masu neman suna da mu za su ce mana kule, za mu ce masu cas.

“Don haka daga yanzu duk wanda ya ke tunanin zai ci mana zarafi, to mu ma ‘yan ƙasa ne, sai dai kotu ta raba mu da shi!

“Mu ba mu san wata sana’ar da ta wuce yin fim ba, mu shi mu ka karanta kamar yadda ake karanta likitanci ko sanin ilimin magunguna ko injiniya ko lauya da sauran su. Don haka ban ga dalilin da zai sa mutum bai taɓa shigowa cikin mu ya gane wa idon sa zahirin me mu ke yi ba, kawai ka yi ta ɓata mu da sana’ar mu a idon duniya. To gaskiya ba za mu lamunta ba. 

“Wace gudunmawa ku ka bayar wajen faɗakar da mu abin da ku ka gani wanda ba daidai ba?”

Da wakolin mu ya nemi jin ƙarin bayani a game da wannan rubutun nasa, sai Faraga ya ce, “Abin da ke faruwa, ai ka ji labarin wanda ya ke maganganu barkatai a kan ‘yan, wanda Alhaji Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya kai shi kotu. Kishin abin ne wallahi ya sa na yi wannan rubutun, kuma na ke ja wa jama’a kunne lallai su san cewa mu ma mu na da masu ilimi waɗanda idan su ka yi mana abu ba za mu iya bari ba.

“Ka ga dai abin da Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya yi abu ne da ake ce wa ‘eye opener’. Da ma duk abin mun yi shiru ne ana kallon mutane ana jin irin abubuwan da su ke faɗa. Kuma mu a harkar tamu akwai abin da mun yi shi ne saboda mu nemi mafita a rayuwar mu, ma’ana ta kasance sana’a a gare mu, ta kasance gatan mu, ta kasance a kowane lokaci ita mu ka sani, ba mu yin wani abu. 

“To duk wanda zai kawo mana cikas, ya kamata mu tsai da shi, mu faɗa masa gaskiya ga inda mu ka doso. Idan  mutum ya na buƙatar ya yi sharhi a kan mu, ya shigo cikin mu, ya zo ya tabbatar da abin da mu ke yi. Idan ya san akwai gyaran da zai yi mana, sai ya yi gyara ya ce abin da ku ke yi ba shi ne mafita ba, ga abin da ya kamata ku yi. 

“Amma mutum bai shigo cikin mu ba, bai taɓa tambayar yaya mu ke yi ba, sannan kuma ka je ka faɗi abin da kai ba ka sani ba, ai ka ga wannan ba adalci ba ne. In har ka shigo cikin mu ka ba da gyara ka ga ba a yi gyaran nan ba, daga nan sai ka fito ka faɗa wa duniya cewa mutanen nan fa  ga inda su ka dosa, ko kuma ga a kan abin da mu ka ɗora su, amma sun ƙi. Ka ga wannan ‘is understood’. 

“Amma ba ka taɓa bincike ba, ba ka taɓa shigowa cikin mu ba, kawai sai ka tafi gidan jarida ko kuma ka faɗa wa duniya cewa ai mu  na gurɓata tarbiyya ko kuma abu makamancin wannan. Wannan bayanin da na yi shi ne matashiya a kan wancan rubutun da na yi.”

A kan maganar ‘yan Kannywood masu ja masu zagi da cin mutunci kuwa, cewa ya yi, “Abin da ke faruwa a yanzu, za ka ga ba ɗan masana’antar Kannywood ba ne kaɗai ya ke yi ya ke tura wa duniya. Su kuma duniya abin da su ka sani kawai Kannywood. 

“To yanzu akwai tsari da aka fito da shi na rijistar duk wani ɗan Kannywood, in dai halastaccen ɗan Kannywood ne, dole sai ya yi wannan rijista da dokoki za su baibaye shi, wanda babu dama ya yi wani abu shi kaɗai, dole  sai da sanin mahukunta na  masana’antar. 

“Kawai ɓatagarin da mu ke da su su ne waɗanda su ba su cikin mu, amma kuma duniya ta ɗauka cewa ‘yan Kannywood ne. To su ba su san menene shugabanci ba, ba su san darajar shugabanci ba, shi ya sa ka ga duk abubuwan da ke faruwa su na yin shi gaba-gaɗi.

“Amma ina wadda ta ke cikin masana’antar Kannywood za ta samu dama ta je ta riƙa yin TikTok ko ta na yin abin da ta ga dama ko ta faɗi abin da ta ga dama? Ka ga ko ai dole shugabanci ya yi aiki a kan ta. 

“Saboda haka yanzu duk wanda ka ga ya na fim, lallai ya bi ‘proper channel’ na rijista, wanda gwamnati ta san da shi, dukkan ‘yan ƙungiya sun san da shi.”

Loading

Tags: ɓatanciHamisu Iyan-TamajarumaiKannywoodTijjani Faraga
Previous Post

2023: INEC ta gargaɗi jam’iyyu da ‘yan takara su yi taka-tsantsan da Dokar Zaɓe ta 2022 a lokutan kamfen

Next Post

Pantami ya naɗa jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi jakaden Hukumar Shaidar Ɗan Ƙasa

Related Posts

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko
Labarai

Wani maigida na ya ce wahalar banza nake yi a kan Yerima Shettima, inji Hussaini Danko

June 13, 2025
Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika
Labarai

Jarumin Kannywood, Abdul M. Shareef zai auri jaruma Maryam Malika

June 12, 2025
Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah
Labarai

Hukumar Tace Finafinai ta Kano ta yaba wa ɗakunan taruka bisa bin doka da oda lokacin bukukuwan Sallah

June 12, 2025
Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna
Labarai

Rahama Sadau ta raba barka da Sallah ga ‘yan fim na Kaduna

June 11, 2025
‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake
Labarai

‘Aure tsakanin jaruman Kannywood, Mansurah da Momoh’: Yadda lamarin yake

June 11, 2025
An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN
Labarai

An naɗa Shehu Hassan Kano shugaban riƙo na MOPPAN

June 3, 2025
Next Post
Nuhu Abdullahi (a dama) tare da shugaban NIMC, Injiniya Aliyu A. Aziz, a ofishin sa a Abuja

Pantami ya naɗa jarumin Kannywood Nuhu Abdullahi jakaden Hukumar Shaidar Ɗan Ƙasa

Comments 2

  1. Pingback: Tabbas Ga masu bata sunan ‘yan Kannywood: Duk wanda yace kule, za mu ce cas!, a cewar Tijjani Faraga. - AppSoft.Com.Ng
  2. Pingback: Wasu Mazan Sai A Hankali! Mijina Yana Saduwa Dani Kamar Daga Yau Shikenan Wata Mata Ta Kai Karar Mijinta - Mr ATG News.com

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!