GWAMNA Abdullahi Umar Ganduje ya yaba wa dattawan masana’antar shirya finafinai ta Kannywood bisa ƙoƙarin su na wayar wa da al’umma kai kan muhimmancin biyan haraji.
Ya faɗi hakan ne a lokacin da dattawan su ka kai masa ziyara a ƙarƙashin ƙungiyar su ta Kannywood Foundation a daren jiya Laraba, 2 ga Yuni, 2021 a fadar gwamnatin jihar da ke Kano.
A lokacin wannan ziyara ta musamman, ƙungiyar ta gabatar wa da gwamnan wani gajeren fim da ta shirya mai suna ‘Da Ruwan Ciki…’
Fim ɗin na nuna yadda ya kamata mutane su riƙa biyan haraji ga gwamnati da yadda za su iya sanin irin ayyukan da gwamnati ke yi da ƙuɗaɗen da su ke biya, musamman ayyukan da su ka shafe su kai-tsaye.
Da ya ke bayyana dalilin shirya fim ɗin a lokacin zaman, babban furodusa Hamisu Lamiɗo Iyan-Tama ya ce, “An yi wannan fim ne domin a ci gaba da yin ayyuka na wayar wa da mutane kai kan abubuwan da su ka shafi haraji, da yadda jama’a ya kamata su bi wajen biyan haƙƙoƙin da ke kan su na haraji, da kuma harkokin tsaro.
“Ya kamata a ce mutane sun ɗauki gaɓar gyara, wanda kuma gwamnati ita kaɗai ba za ta iya ba sai da haɗin kan jama’a.”
A nasa jawabin ne ɓangaren Dakta Ganduje ya yaba tare da bayyana jin daɗin sa bisa wannan hoɓɓasa da dattawan na Kannywood su ka yi na nusar da al’umma kan muhimmancin biyan haraji.

Kazalika ya ce wannan aiki ya na matsayin wani tsani da zai taimaka wa jama’a su fahimci yadda ake gudanar da kuɗaɗen da gwamnati ta ke karɓa na haraji a faɗin jihar.
Bugu da ƙari, ya hori dattawan da su ƙara ƙaimi wajen shirya irin waɗannan finafinai da za su hasko wa jama’a wani abu da ya shige musu duhu game da gwamnati.
Ya bada misali da cewa, “Kamata ya yi ana shirya irin waɗannan finafinan, musamman ga masu babura masu ƙafa uku, wato Adaidaita Sahu, don sanin muhimmancin titunan da ake musu su na hawa domin yin kasuwanci ta hanyar bada kuɗin haraji.
Ya ce, “A kuma maida hankali wajen faɗakarwa kan tsaro, duk da ba za a iya nunawa ba amma ya kamata mutane su gane cewa yayin da su ke kwance su na barci, jami’an tsaro fa ba barci su ke ba.”
A ƙarshen jawabin sa, gwamnan ya yaba da sadaukarwar da ƙungiyar ta yi domin shirya wannan fim da kuma mallaka shi ga gwamnatin jihar kyauta ba tare da ta biya su ba.
Bayan kammala kallon fim ɗin, su ma kwamishinonin jihar da dama sun yaba da yadda aka tsara fim ɗin tare da bada shawarwari a wuraren da aka samu kurakurai a cikin sa.
Dattawan Kannywood da su ka halarci zaman nuna fim ɗin sun haɗa da Shu’aibu Yawale, Auwalu Isma’il Marshal, Ɗan’azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa (Kamaye), Hamisu Iyan-Tama, Dakta Ahmad Sarari, Bala Anas Babinlata, Hajiya Balaraba Ramat Yakubu, Ali Sambo, Balarabe Tela da kuma Khalid Musa.

