GWAMNA Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya naɗa babban furodusan finafinan Hausa Alh. Abdallah Tahir Al-Kenanah matsayin Darakta-Janar na Hukumar Ƙawata Birane.
Al-Kenanah dai shi ne Mataimakin Shugaban ƙungiyar masu shirya finafinai ta Arewa kuma mai bincike na 1 a ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kano.
A wata sanarwa da ta fito daga gidan gwamnati a yau Juma’a ɗauke da sa-hannun Sakataren Yaɗa Labarai na gwamna, Malam Abba Anwar, an bayyana cewa gwamnan ya bayyana gamsuwar sa da yadda Al-Kenanah ya sadaukar da rayuwar sa wajen aikin ƙawata birnin Kano a wannan lokaci.
Ganduje ya ce masa, “Ka ci gaba wannan kyakkyawan aikin, don a kai aikin ƙawata biranen mu zuwa mataki na gaba.”
‘Yan fim da dama sun taya furodusan murna.
Mataimakin Sakatare-Janar na ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa, Malam Salisu Mohammed Officer, ya yi addu’ar “Allah Ubangiji ya sa wannan masana’anta ta ƙaru da wannan muƙami.”
Sannan ya yi kira ga ‘yan’uwan sa ‘yan fim da su taya shi da addu’ar samun nasara.