ƘUNGIYAR Ƙwararru Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN) ta bayyana godiya ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa ɗaukar nauyin wasu daga cikin membobin ta domin gudanar da aikin Hajjin 2025.
A wata wasiƙa da mai magana da yawun ƙungiyar, Ibrahim Amarawa, ya sanya wa hannu, MOPPAN ta yaba da wannan alheri daga gwamnatin jihar, tana mai cewa hakan alamar goyon baya ne ga masana’antar Kannywood da ma’aikatanta.
Cikin waɗanda suka amfana da tallafin akwai Hajiya Fauziyya D. Sulaiman, Umar UK, TY Shaba, Garzali Miko da KB International.
“Wannan karamci da ka nuna ya ƙara tabbatar da cewa kana da cikakken kishin bunƙasa masana’antar Kannywood da walwalar waɗanda ke aiki a cikin ta,” inji ƙungiyar a cikin wasiƙar.
Ƙungiyar ta bayyana jin daɗin ta da irin jagoranci nagari da manufofin ci gaba da gwamnatin Gwamna Yusuf ke aiwatarwa, wanda ta ce yana ci gaba da inganta harkar nishaɗi a Kano.
“Muna addu’ar Allah (SWT) ya saka maka da alheri, ya ƙara maka basira da ƙarfin guiwa domin ci gaba da jagorantar al’amuran Kano cikin nasara tare da ci gaba da tallafawa Kannywood,” inji MOPPAN.
Ƙungiyar ta kuma jaddada ƙudirin ta na ci gaba da aiki tare da gwamnatin jihar domin haɓaka masana’antar ƙirƙira da nishaɗi a faɗin Kano.