HUKUMAR Tace Finafinai Da Ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da sayar da littafin ‘Queen Primer’, tare da kira ga malaman makarantu masu zaman kan su da su guji amfani da su.
Littafin na cikin jerin wasu littattafai da ake amfani da su a makarantun jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya yi a ofishin sa a jiya Alhamis, inda ya ce, “Wannan lamari abin dubawa ne, saboda ankarar da jama’a da wasu masu nazari su ka yi a game da wasu abubuwa na ɓata tarbiyya da ya ke ƙunshe a cikin littafin.
“Don haka mu a matsayin mu na masu kare tarbiyya da hana yaɗuwar ɓarna mu ka ɗauki wannan mataki na dakatarwa.”
Babban sakataren ya ƙara da cewa, “Don haka mu na kira ga malamai da kuma shugabannin makarantu da su guji amfani da wannan littafi domin kuwa duk wanda aka kama da su doka za ta yi aiki a kan sa.”

Mujallar Fim ta ruwaito cewa a ‘yan kwanakin nan wannan littafin ya tayar da ƙura a soshiyal midiya, inda ta kai har wasu malamai da masana kalmomin Turanci su na ta tofa albarkacin bakin su a kan sa.
Babban abin da mutane ke magana a kai shi ne wai kalmar ‘Queen’ da aka saka a sunan littafin na nufin ‘luwadi ɗi’ a wani ƙaulin.
Wata takarda da aka saki daga ofishin mai ba Gwamna shawara kan makarantu masu zaman kan su, Comrade Baba Abubakar Umar, ta lissafa littattafai shida da gwamnatin ta hana amfani da su a makarantun jihar.
Kamfanin Evans Publishers shi ne ya wallafa littafin domin a yi amfani da shi a ƙananan makarantu.