HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta dakatar da duk wani aikin shirya fim a jihar har tsawon mako biyu.
Wannan dakatarwar ta biyo bayan fara sabunta tantancewa da rajistar lasisin ‘yan fim.
Hukumar ta ba da wannan sanarwar ne a jiya Litinin, 11 ga Satumba, 2023 inda ta soke lasisin duk wani mai hulɗa da ita daga farkon hawan sabon Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha.
Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya ce a cikin sanarwar: “Za a gudanar da sabunta rajistar ne a ƙarƙashin Hukumar Tace Finafinai da Ɗab’i tare da haɗin gwiwar MOPPAN, Arewa Film Makers da Kannywood Elders Forum.”
Ya ƙara da cewa dukkan ƙungiyoyin ‘yan fim, wato ‘guilds’, ban da kamfanoni na Kannywood, za su je wajen yin rajistar.
Ya ce wannan dama ce ga masu son yin rajista da hukumar, wanda a baya ba su samu damar yin rajistar da hukumar ba.
Masu harkar fim da dakatarwar ta shafa sun haɗa da masu fassarar finafinai, masu kyamara, masu editin, masu waƙa,’yan dawunlodin, masu gidan gala, masu tallar magani, masu ɗaukar hoton kati, masu DJ, daraktoci, ‘yan wasa, masu kula da fitila a wajen shutin, marubuta da masu tsara labari, masu shagunan tsara fosta (cafe), da sauran duk masu abokan hulɗar hukumar waɗanda ba su ga sunan su a cikin sanarwar ba.
Za a gudanar da tantancewa da rijistar a ofishin ƙungiyar MOPPAN reshen Jihar Kano da ke Titin BUK.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa a halin yanzu dai duk masu ɗaukar fim a Kano za su dakatar da ayyukan su har sai an kammala aikin tantancewa da rajistar.
Comment:ok hakama yayi