GWAMNATIN Tarayya ta ba fitaccen kamfanin shirya finafinai ɗin nan mai suna Lenscope Media aikin gina Gidan Shirya Finafinai na Jos (wato film village) da haɓaka wasu wuraren tarihi da ke Kano, Katsina da Zariya.
Za a gina Gidan Shirya Finafinai ɗin ne a wani ɓangare na haɓaka Gidan Tarihin Gine-ginen Gargajiya na Jos, wato Museum of Traditional Nigerian Architecture (MOTNA).
A cikin aikin haɓaka wuraren tarihin, Lenscope Media za su sake gina muhimman wuraren tarihi irin su Badalar Birnin Kano, da Masallacin Juma’a na Zariya, da Fadar Sarkin Katsina, waɗanda a da ana amfani da su a finafinan da aka shirya a Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare.
Yanzu za a lissafa waɗannan wuraren tarihin a cikin ababen da ke ƙarƙashin Gidan Shirya Finafinai na Jos domin inganta wuraren da ake gani a cikin finafinai tare da taskace wuraren tarihi na gargajiya.
Hukumar Gidajen Adana Kayan Tarihi Da Wuraren Tarihi ta Ƙasa (National Commission for Museums and Monuments, NCMM) ita ce ta ba da kwangilar.
Hukumar da kamfanin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar aikin a ranar Alhamis a Abuja.
Shugaban Lenscope Media, fitaccen jarumi Makama Sani Mu’azu, shi ne ya rattaba hannu a madadin kamfanin sa, shi kuma Darakta-Janar na hukumar, Mista Olugbile Holloway, ya rattaba hannu a madadin Gwamnatin Tarayya, yayin da Lauya Babatunde Adebiyi ya jagoranci rattaba hannun a taron.
Yarjejeniyar dai irin ta haɗin gwiwar gwamnati da kamfani mai zaman kan sa ce, wato Public-Private Partnership (PPP), kuma za ta shafe tsawon shekara 20.
Ana sa ran aikin zai sauya fasalin Gidan Tarihin na Jos zuwa sabon Gidan Shirya Finafinai na Jos da kuma Makarantar Koyon Shirya Fim, wato Film Training School.
Hakan zai ƙara tabbatar wa da Jihar Filato da matsayin ta na cibiyar inganta harkar fim.
Alhaji Sani Mu’azu ya sha alwashin cewa kamfanin sa zai yi amfani da ɗimbin sanin makamar aiki da yake da shi wajen dawo da martabar waɗannan wuraren tarihin da kuma sauya fasalin abin da za a riƙa yi a cikin su ta fuskar ayyukan fasaha.
Ban da batun shirya fim ma, sabon Gidan Shirya Finafinai na Jos ɗin zai ƙunshi Gidan Cin Abinci na Arewa inda za a samu abincin gargajiya iri-iri na arewacin Nijeriya, da kuma kayan hawan doki daban-daban domin yin amfani da su a finafinai, wanda hakan zai jawo mashirya fim da masu yawon buɗe ido zuwa wurin.
Kuɗin farko da aka zuba a kwangilar shi ne naira miliyan ɗari biyu da hamsin (₦250m), wanda ake sa ran zai haɓaka tattalin arzikin inda za a yi aikin, zai samar da aikin yi ga dubban matasa masu basira, kuma ya ƙarfafa matsayin Jihar Filato na babban wurin da mashirya fim daga sassan Afrika suke zuwa domin shirya fim.
Ana sa ran cewa idan har Gidan Shirya Finafinai na Jos ɗin ya fara aiki, zai inganta yadda ake shirya fim, ya haɓaka al’adun gargajiya, kuma ya haɓaka harkar yawon buɗe a Nijeriya.
Kamfanin Lenscope Media ya bayyana wannan al’amari da sunan “muhimmin cigaba ga masana’antar fim ta Nijeriya”.