• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tarayya ta yi fatali da zargin da Peter Obi ya yi mata kan ɗorin kasafin kuɗi

by DAGA WAKILIN MU
November 10, 2023
in Nijeriya
0
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ɗorin kasafin kuɗi na shekarar 2023 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu a ranar Laraba, 8 ga Nuwamba, 2023 ba a yi shi cikin rashin tunani da hangen nesa ba, an yi shi ne bisa la’akari da halin matsin tattalin arziki wanda Nijeriya ta ke fuskanta a yanzu. 

A wata takarda ga manema labarai da ya rattaba wa hannu a ranar Alhamis, hadimin ministan na musamman a ɓangaren yaɗa labarai, Malam Rabi’u Ibrahim, ya ruwaito cewa ministan ya yi kira ga ɗan takarar zama shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya samu lokaci ya zauna ya karanta kundin ɗorin kasafin kuɗin na naira tiriliyan 2.17 a tsanake domin ya fahimce shi da kyau, zai ga ya ƙunshi tanadin kuɗin da aka yi wa muhimman ayyuka irin su tsaro, aikin gona, wadata ƙasa da abinci, ayyuka da gidaje, ƙarin albashi ga ma’aikata, shirin bada rance ga ɗalibai, da hanyoyin sauƙaƙa wa talaka halin da ya ke ciki, da sauran su, waɗanda an yi su ne don a ƙarfafa ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar tare da inganta halin zamantakewa a tsakanin ‘yan Nijeriya.

Ya ce: “Ɗimbin tanade-tanaden da ke cikin ɗorin kasafin kuɗin ya nuna babban burin Shugaba Tinubu da yadda ya ke matuƙar son ya tallafa wa ayyukan da gwamnati ta sa a gaba, ya tunkari matsalar tsaro gaba-gaɗi, kuma ya gaggauta haɓaka hanyoyin da za a bi a magance matsalolin ƙasar waɗanda cire tallafin mai ya haifar.

Idris ya yi kira ga ‘yan siyasar adawa da su kasance masu sani kuma adalai wajen bayyana ra’ayin su mabambanta, sannan su kauce wa yi wa gaskiya jirwaye don kurum su cimma burin siyasa. 

Ya yi bayanin cewa an yi ɗorin kasafin kuɗin ne bayan tattaunawa tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki da su ka dace waɗanda su ka bada tabbacin cewa kasafin ya yi daidai da buƙata da muradun jama’ar Nijeriya.

Idris ya nanata cewa kamar yadda Shugaba Tinubu ya ke da son ganin an bi dukkan ƙa’idoji wajen sarrafa kuɗin gwamnati, to sai da aka yi nazari a tsanake kan kowane lissafi a kasafin kuɗin don tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen jama’a a yadda ya kamata.

Loading

Previous Post

Marubuciyar farko a Arewa, Hajiya Hafsatu Abdulwaheed, ita ce baƙuwar marubuciyar ƙungiyar ANA Abuja ta watan Nuwamba

Next Post

‘Yan Kannywood sun nuna wa Hisbar Kano yatsa kan gayyatar su da ta yi

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Daga hagu: Alhassan Kwalle da Umar U.K.

'Yan Kannywood sun nuna wa Hisbar Kano yatsa kan gayyatar su da ta yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!