HUKUMAR Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa (NFVCB) ta gargaɗi ‘yan fim da mawaƙan Hausa da su daina sakin finafinai ko waƙoƙin su a YouTube ba tare da amincewar hukumar ba.
Wannan gargaɗin ya fito ne daga bakin jami’in hukumar mai kula da yankin Arewa-maso-yamma, Malam Umar G. Fage, a cikin wata takarda da ya aika wa ‘yan fim da mawaƙa a ranar Litinin, 15 ga Fabrairu, 2021.
A takardar, wadda ya rubuta a madadin Babban Daraktan hukumar, wato Alhaji Adedayo Thomas, jami’in ya ce: “Mu na sane da cewa wasu daga cikin furodusoshi su na sakin finafinai da bidiyon waƙoƙi a yanar gizo ta hanyar ƙirƙirar tasha a sanannen gidan yanar nan inda ake ɗora bidiyo mai suna YouTube ba tare da tacewar hukumar ba, wanda hakan ya saɓa wa sashe na 5 (1), 33 (1) na dokar hukumar ta 1993, cap. N40 LFN 2004 da kuma Dokar 2008.
“Don haka hukumar ta na kira a gare ku da ku kiyayi yin hakan, kuma ku riƙa miƙa finafinan ku da bidiyon waƙoƙin ku ana tace su saboda kada ku gamu da fushin doka.”
Tun da farko a takardar tasa, kuma mujallar Fim ta samu kwafe, sai da Umar G. Fage ya ja hankalin dukkan furodusoshin fim da masu shirya bidiyon waƙoƙi da masu nuna finafinai da ‘yan kasuwar fim da su lura sosai da abin da dokar da ta kafa hukumar ta tanada.
Ya ce doka mai taken ‘Cap. No. LFN 2004’ da ‘Regulations 2008’ wadda a da ake kira ‘Decree No. 85 of 1993’ su ne su ka samar da Hukumar Tace Finafinai da Bidiyo ta Ƙasa da ikon sanya ido kan dukkan harkokin masana’antar shirya finafinai da bidiyo a Nijeriya.
“Saboda haka aikin hukumar ne ta ba mutum lasisin nuna ayyukan fim da bidiyo da kuma wajen da za a riƙa nuna ayyukan finafinai da bidiyo.
“Ban da waɗannan ayyukan, an ba hukumar hurumin ta tace ayyukan finafinai da bidiyo kuma ta ba su lambar ajin da ya kamata su zauna, sannan ta aiwatar da irin waɗannan ayyukan kamar yadda aka lissafa su a dokar da ta kafa hukumar.”
Idan kun tuna, a kwanan baya ma sai da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta bada umarnin a daina sakin finafinai ko waƙoƙi a YouTube ba tare da an kai mata su ta tace su ba.
Shugaban hukumar, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah), ya yi barazanar cewa hukumar tasa za ta hukunta duk wanda aka kama da bijire wa wannan umarnin.
Sai dai har ya zuwa yanzu mujallar Fim ba ta ji an fara ɗaukar mataki a kan masu sakin finafinan da waƙoƙin ba tare da hukumar tasa ta tace su ba.

Me gwwamnati tayiwa yan film din hausa da zamu biya kudi dan tace abinda zamu sa a youtube ai youtube ba na Nigeria bane dan haka baza muyi ba