• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

Gwamnatin Tinubu za ta sake zuba kuɗin da ake tarawa daga janye tallafin wutar lantarki wajen inganta lantarki, kiwon lafiya, da ilimi – Idris

by WAKILIN MU
April 14, 2024
in Nijeriya
0
Gwamnatin Tinubu za ta sake zuba kuɗin da ake tarawa daga janye tallafin wutar lantarki wajen inganta lantarki, kiwon lafiya, da ilimi – Idris

Minista Alhaji Mohammed Idris (a dama) tare da Shugaban FRCN Kaduna, Malam Buhari Auwalu, a lokacin gudanar da shirin "Hannu Da Yawa"

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram
Minista Alhaji Mohammed Idris (a dama) tare da Shugaban FRCN Kaduna, Malam Buhari Auwalu, a lokacin gudanar da shirin “Hannu Da Yawa”

MINISTAN Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sama da naira tiriliyan 1 da za a tara daga janye tallafin wutar lantarki za a sake zuba su ne wajen inganta wutar lantarki, kiwon lafiya, da ilimi ga ‘yan Nijeriya.

Da yake jawabi a matsayin babban baƙo na shahararren shirin Rediyo Nijeriya na Kaduna mai suna ‘Hannu Da Yawa’ a ranar Asabar a Kaduna, Idris ya ce a kusan kashi 40 na tallafin wutar lantarki, kashi 15 ne kawai masu amfani da wutar lantarki ke amfana wanda ya ƙunshi mawadata da gungun masana’antu, waɗanda ke jin daɗin wutar lantarki na kusan awanni 20.

Ya ce, “Yana da muhimmanci a jaddada cewa kuɗaɗen da za a ajiye daga janye tallafin wutar lantarki, za a sake zuba su ne wajen inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar nan da inganta sauran muhimman ayyukan jama’a kamar kiwon lafiya da ilimi. Kusan kashi 85 cikin ɗari na al’ummar da ke cikin sabon tsarin samar da wutar lantarki har yanzu suna samun tallafin.”

Ministan ya ce sabuwar dokar samar da wutar lantarki da Shugaban Ƙasa Tinubu ya sanya wa hannu ta ƙara ƙarfafa tsarin gudanar da ayyukan Hukumar Kula Da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) tare da bai wa hukumar damar sanya wa kamfanonin rarraba wutar lantarkin (DISCOs) tsauraran takunkumi kan laifukan da suka shafi kuɗi da samar da wutar ga masu amfani.

Idris ya kuma bayyana cewa kwamitin da Shugaban Ƙasa ya kafa domin duba tsarin tafiyar da Shirin Zuba Jarin Jama’a na Ƙasa ya gabatar da rahoton sa domin share fagen sake gudanar da shirye-shiryen, wanda zai bayar da tallafin kuɗi naira 25,000 ga talakawa miliyan 15 da magidanta masu rauni na tsawon watanni uku a tsakanin sauran ayyukan.

Ministan, wanda ya yi amfani da wannan dandali wajen kawar da maganar da wasu ke yi cewa wai gwamnatin Tinubu na shirin cutar da arewacin ƙasar nan, ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da zuba kuɗaɗe wajen bunƙasa ayyuka a Arewa.

Ya yi nuni da cewa gwamnatin ta faɗaɗa noman alkama, shinkafa, rogo, da masara, a ƙarƙashin Shirin Noman Rani zuwa kadada 500,000 na gonaki.

Ya ce: “Shugaban Ƙasa ya umarce mu da mu fito mu ji halin da al’umma ke ciki, mu kawo masa rahoto. Mun je Dutse, Auyo, da Haɗeja, kuma mun tattauna da manoma game da nasarorin noman rani a waɗannan yankuna”.

Idris ya bayyana jin daɗin sa kan yadda a yanzu Jihar Kebbi ta zama cibiyar noman tumatur da sarrafa tumatur a ƙasar nan ta hanyar haɗin gwiwa da wani babban kamfanin sarrafa abinci mai suna GB Foods, wanda ya kafa wata masana’anta domin noman tumatur.

Ya ce manoma da dama, waɗanda galibin su mata ne, yanzu haka su na noman tumatur a Jihar Kebbi, saboda yanayin da ake samu da kuma tallafi daga GB Foods, wanda ya nuna matuƙar jajircewa wajen yin kasuwanci a Nijeriya.

Loading

Tags: Buhari AuwaluFRCN Kadunagwamnatin TinubuHannu Da YawaMohammed Idris
Previous Post

Ƙungiyar matasa da mata za ta naɗa Ado Gidan Dabino Sarkin Mawallafan Arewa

Next Post

Shekaru goma bayan sace ‘yan matan Chibok: Nijeriya ba za ta ƙara biyan kuɗin fansa ba

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shekaru goma bayan sace 'yan matan Chibok: Nijeriya ba za ta ƙara biyan kuɗin fansa ba

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!