A JIYA Lahadi, 4 ga Satumba, 2022 Allah ya ɗauki ran mahaifiyar fitaccen gwanin rawa kuma mawaƙi Abdul S. Tynking Maigashi.
Mahaifiyar tasa, Hajiya Safiya Hussaini Sabo, ta rasu da misalin ƙarfe 6:00 na safe a wani asibiti mai suna Oshegba Hospital a garin Lafiya, Jihar Nassarawa, sakamakon ciwon suga da ta yi fama da shi na tsawon shekara bakwai.
An yi mata sallah a gidan ta da ke Gonar Shalele, a Lafiya.
Tynking Maigashi ne na tara a cikin ‘ya’yan ta.

Mujallar Fim ta ruwaito cewa ‘yan fim da su ka je masa ta’aziyya sun haɗa da Abubakar S. Shehu, Ahmad Shanawa, Sadiq Shanawa, Umar Bigshow, Zainab Sambisa, da Suhailat Ishaq. Waɗanda su ka kira shi a waya kuma sun haɗa da Abdul Amart Maikwashewa, Umar M. Shareef, Sadiq Mafia, Ɗanmusa Gombe, Hamisu Breaker, Haruna Talle Maifata, Hamza Talle Maifata, Teema Yola, Fati S.U. Garba da sauran su.
Allah ya jiƙan Hajiya Safiya da rahama, amin.
