MINISTAN Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya karɓi baƙuncin abokan aikin sa biyu, wato
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, da Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle, a ofishin sa, jiya a Abuja.
Sun yi tattaunawa mai alfanu kan hanyoyin inganta ayyukan samar da tsaro da jinƙai na gwamnatin Shugaba Tinubu.
