MAWAƘI a Kannywood, Ali Isa Jita, ya yi wa dukkan al’ummar Musulmi addu’ar Allah ya ba su damar ziyartar Ƙasa Mai Tsarki.
Ali ya yi wannan addu’ar ne yayin da ya ɗora wasu hotuna a Instagram tare da matar sa da ‘ya’yan sa biyar, maza uku, mata biyu, daga birnin Makka.
A ƙasan hotunan, ya yi rubutu da Turanci, inda ya ce, “Alhamdu lillah. Blessed to parform Umrah with family. May Allah accept it, ameen. May Allh bless all muslims to visit once in life to most beautiful & blessed place on earth, Makka. Masu saƙon addu’a, mun isar da saƙon ku.”
Mujallar Fim ta fassara rubutun da cewa: “Na gode wa Allah, albarka ne yin Umrah tare da iyali. Allah ya karɓa mana, amin. Allah ya albarkaci dukkan Musulmi su ziyarci mafi kyawun wuri da albarka a ƙasa, wato Makka.”
Ya kuma ce, “Masu saƙon addu’a, mun isar da saƙon ku.”
Waɗannan hotuna sun ɗauki hankalin jama’a matuƙa a soshiyal midiya, don tun bayan da Ali ya ɗora su, abokan sana’ar sa da masoya su ma su ka ci gaba da rabawa a shafukan su tare da yi masu fatan alheri.