MANAJAN Darakta na Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), Alhaji Ali Nuhu, ya gana da wakilan kamfanin Netflix da ke da babban ofishi a garin Amsterdam na ƙasar Nezalan a ranar Talata, 5 ga Maris, 2024 a ofishin sa da ke Abuja.
Ali Nuhu da wakilan na Netflix sun tattauna batutuwa ne kan yadda za a bunƙasa hukumomin shirya finafinai da ke kudanci da arewacin Nijeriya.
Netflix sun ci alwashin ba da gudunmawa ɗari bisa ɗari don ganin harkokin finafinai sun haɓaka ta ɓangaren su tare da jaddada goyon baya ga duk wani abu da ya danganci sabon shugabancin wannan hukuma ta finafinai da ke wannan ƙasa.
Bayan ganawa da tawagar, Ali ya yi taƙaitaccen bayani da Turanci a kan tattaunawar tasu a soshiyal midiya, mujallar Fim ta fassara zuwa Hausa.
Ali ya ce, “A matsayi na na Manajan Darakta na Hukumar Finafinai ta Nijeriya, na yi imani da gaske game da sauye-sauyen damar finafinai don daidaita al’adu, haifar da tattaunawa, da kuma ƙarfafa canji.

“Ganawa ta da Netflix alama ce ta haɗin gwiwa don haɓaka muryoyi da labarai daban-daban, yin amfani da harshen finafinai na duniya don murnar haɓakar al’adun Nijeriya a fagen duniya.”
Ali ya ci gaba da cewa, “A tsakiyar wannan haɗin gwiwar ya ta’allaƙa ne da sadaukar da kai ga sahihanci da haɗa kai.
“Mun fahimci muhimmancin kiyaye mutuncin labaran Nijeriya tare da rungumar damar da dandalin intanet ke bayarwa ta hanyar yin aiki hannu da hannu tare da Netflix.
“Mu na nufin ƙarfafa wa masu yin finafinai na gida, samar masu da albarkatu da tallafin da ake buƙata don kawo hangen nesa na rayuwa.
“Tare za mu iya ƙalubalantar ra’ayi, wargaza rashin fahimta, da kuma nuna kyau da sarƙaƙiyar al’ummar Nijeriya ta kowane fanni.
“Yayin da mu ka fara wannan tafiya ta binciken ƙirƙire-ƙirƙire, mu na ci gaba da lura da alhakin da aka ɗora mana.
“Bayan nishaɗi, sinima ya na da ikon tada tunani, haifar da tausayawa, da ƙarfafa aiki ta hanyar haɗin gwiwar mu da Netflix.

“Mu na burin kunna tattaunawa mai ma’ana, haɓaka fahimta, da share hanya don ƙarin haɗaɗɗiyar duniya da tausayi, tare, za mu iya amfani da ikon canza labarai don ƙirƙirar makoma mai haske, mai bege ga tsararraki masu zuwa.”
A ɓangaren Netflix, sun yi alƙawarin ba da dama ga duk wasu manya-manyan kamfanoni da su ke wannan ƙasa don ganin cewa su ma sun baje kolin hajar su a kasuwar finafinai ta duniya.
Haka kuma sun yi murna ƙwarai da gaske da wannan matsayi da Ali ya samu, ganin cewa an aje ƙwarya a gurbin ta.
Sun kuma gamsu da cewa wannan sabon shugaba da aka kawo shi ne cikakken wanda zai kai wannan hukuma zuwa mataki na gaba.
