HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab’i ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ta Alhaji Abba El-Mustapha ta ƙaddamar da kwamitin mutum goma a kan gasar ƙirƙirarrun labari da ta saka.
A wata sanarwa ga manema labarai da Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar, Malam Abdullahi Sani Sulaiman, ya sa wa hannu, wanda mujallar Fim ta samu kwafe, hukumar ta ce Babban Sakataren hukumar, Alhaji Abba El-Mustapha, shi ne ya ƙaddamar da kwamitin.
Wannan shi ne karo na farko da hukumar ta saka irin wannan gasar tun da aka kafa ta a cikin 2001.

A wajen ƙaddamar da kwamitin a zauren taron hukumar, El-Mustapha ya bai wa kwamitin alhakin kula da dukkan ayyukan gasar tun daga farko har zuwa ƙarshe.
Ya kuma buƙaci mafi girman goyon baya da haɗin kai domin cimma manufofin da aka gindaya.
El-Mustapha ya yi addu’a ga Allah da ya bai wa kwamitin hikima da jajircewa wajen gudanar da aikin tare da yi wa ’yan takarar fatan samun nasara a gasar tare da samun sakamako mai kyau.

Yayin da ta ke jawabi a wurin taron, Dakta Halima A. Ɗangambo, wadda malama ce a Sashen Harsunan Nijeriya a Jami’ar Bayero, Kano, ta yi kira ga Hukumar Tace Finafinan da ta haɗa hannu da jami’ar a gasar, inda ta ce yin hakan zai taimaka ƙwarai da gaske ga hukumar ta cimma ƙudirorin da ta sa a gaba.
Membobin kwamitin dai su ne:
- Farfesa Ahmad Magaji (BUK)
- Dakta Halima A. Ɗangambo (BUK)
- Malam Kamilu Ɗahiru Gwammaja (BUK)
- Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, MON
- Malama Fauziyya D. Sulaiman
- Ɗan’azimi Baba Ceɗiyar ‘Yangurasa
- Hajiya Balaraba Ramat Yakubu
- Abubakar Zakari G/Babba
- Isah Abdullahi Haruna
- Iliyasu Garba
