SHAHARARREN mawaƙin siyasa, Alhaji Ibrahim Sale (Yala), ya bayyana cewa a cikin matan sa uku kaf babu mai haƙuri da kau da kai da juriya kamar uwargidan sa, wato Malama Nafisa.
A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da mawaƙin kan cikar su shekara 25 da aure jiya, Yala ya fara da yi wa Allah godiya, inda ya ce, “Alhamdu lillahi, alhamdu lillahi, alhamdu lillahi, domin ko babu komai Allah ya raya ka ka cinye wajen kwata na ƙarni a aure, ma’ana shekara 25, wannan wani godiya ne ga Allah s.w.t., kuma cikin zaman lafiya da so da ƙauna, sai dai abin da ba za a rasa ba a matsayin mu na ‘yan’adam.
“Kuma sirrin wannan zama na aure tsakani na da uwargida na Nafisa, ƙauna ce. Don gaskiyar magana ita ce an buga soyayya. Mun so juna tsakani da Allah, har Allah s.w.t. ya ƙaddara mu ka yi aure.
“Kuma ni dai a iya tunani na, akwai mace da zan iya samu, ban tara sani ga Allah ba, abin da na sani na zahiri tunda ina da mata guda uku, amma babu wadda ta kai Nafi uwargida na haƙuri da kau da kai da juriya a rayuwa.
“Wannan ya na daga cikin sirrin zamantakewar mu da kuma daɗewa da ka ga mun yi mu na zama a matsayin mata da miji.
“Ta mai da ni ɗan’uwan ta, na mai da ta ‘yar’uwa ta, kuma mu na zaman shawara na rayuwa. Komin ɓacin rai, in-sha Allahu Rabbi sai ka ga an samu masalaha an zauna ana yin abin da ya dace. Wannan shi ne babban sirrin mu.”

Yala ya ci gaba da cewa, “Sannan Allah ya azurta mu da ‘ya’ya guda takwas. Ta farko ita ce Sa’adatu, ita ce babbar ‘ya ta, amma Allah s.w.t. ya yi mata rasuwa bayan ta yi aure, ranar da ta haifi ‘ya mace ranar Allah ya ɗauki rayuwar ta. Wanda yanzu haka ‘yar a matsayin ta ta jika ta tunda aka haife ta ‘direct’ gida na aka kawo ta, Kakar lokacin ta gama shayarwa kenan ba daɗewa ta sake mai da ta a nono.
“Sannan akwai Hauwa’u, ina kiran ta da Ummi. Akwai Muhammad Auwal, Muhammad Nura, Usman, Faɗima, Maryama, sai Aminatu.
“Haihuwar ta takwas Nafisa, kuma ɗaya ce Allah ya ɗauki ran ta bayan ta yi aure a wurin haihuwa kamar yadda na faɗa maka. Kuma ta tafi ta bar ‘ya wadda sunan ta aka mai da mata, Sa’adatu. Na rasa Sa’adatu ‘ya, na samu Sa’adatu jika, wanda ita ma ta zama kamar ‘yar a cikin gida.
“A yanzu mata na uku, ‘ya’ya na 13. Mata ta ta biyu ‘ya’yan mu biyar; akwai Buhari, A’isha, Abdullahi, Abdulhadi da Zainab.
“Mata ta ta uku kuma ta samu ciki aka yi mata aiki, ‘yar ta zo babu rai. Wannan shi ne a taƙaice.
“Yanzu ina da shekara 50 a duniya, kuma ina nan zaune a unguwar Hayin Banki, a nan Allah ya yi zaman.”
Yala ya ba waɗanda ba su yi aure ba wata shawara, inda ya ce, “Shawara ta ga waɗanda ba su yi aure ba, su yi ƙoƙari, kamar yadda Manzon Allah s.a.w. ya ce, ya ku taron matasa, wanda ya samu iko a cikin ku ya yi aure. Aure babban al’amari ne musamman a wannan zamani da mu ke ciki. In mu na son kauce wa sha’awa da faɗawa halaka da masifa na zamani, to aure shi ne mafi a’a’la.
“Kuma shi ne duk wanda aka same shi ta hanyar auren sunna, shi ma ya na so ya samu. Kuma babbar daraja ce da kuma babban alkhairi mutum ya yi aure ya hayayyafa ya samu zuri’a ko da bayan ba shi a raye ya na da masu yi masa addu’a.
“Sannan shawara da zan ƙara bayarwa, musamman ma mu a wannan masana’antar, ya zama wani irin abu kamar yadda na ga wani ya yi ‘posting’ cewa aure ya na riga ankon biki mutuwa, kuma ba ƙarya ba ne.
“Gaskiyar magana shi ne waɗannan masifun da hannayen mu mu ke ƙirƙirar su. Dalili kuwa shi ne za a ɗaura aure bisa sunnar Annabi s.a.w., amma za a yi murnar aure da sunnar sheɗan.
“Za mu kwana, mu wuni a yi kwana kusan uku ana bidi’o’i, mu na cashewa, mu na kaɗe-kaɗe da raye-raye, mu na cuɗanya maza da mata. Wannan ba na cire kai na ba ne, ni ma na taɓa tsintar kai na a cikin wannan yanayin.
“Wallahi tallahi wannan ba ƙaramar masifa ba ce. Wannan ya na ɗaya daga cikin abubuwan da ke rusa aure da albarkar aure.
“Bayan nan kuma, da yawa-yawan mu ana samun haɗuwa, wanda wasu a baya su na fakewa da wata fatawa ne, wanda wannan fatawar ko malaman da su ka kawo ta ma sun kore ta. Don haka yanzu babu wannan fatawar na cewa don ka biya sadaki matar ka ta halasta a gare ka. A’a, ba ta halasta a gare ka ba, sai an ɗaura aure da shaidu.
“Ni shawarar da zan ba dukkan Musulmi, idan Allah ya sa mun samu dama za mu yi aure, in an ɗaura auren bisa sunnar Annabi s.a.w., mu yi murna na wannan aure bisa sunnar Annabi s.a.w.
“Akwai hanyoyi da dama da ake yin murna ba tare da an saɓa wa Allah ba. Wannan shi ne shawara ta.”
A jiya Alhamis, 26 ga Yuni, 2024, Ibrahim Yala da uwargidan sa Nafisa su ka cika shekara 25 da aure.
An ɗaura auren su a ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 1999.