SAKAMAKON ibtila’in kashe-kashe da kidinafin da ya lulluɓe jihohin Arewa, fitacciyar furodusa a Kannywood, Hajiya Mansurah Isah, ta yi kira ga jama’a da su fito su yi taron karatun Alƙur’ani da addu’o’i a ranar Asabar mai zuwa domin neman ɗauki daga Allah s.w.t.
Ta bayyana manufar taron da cewa za a yi shi ne “domin samar wa ƙasar mu zaman lafiya, kwanciyar hankali, shuwagabanni na arziki da alheri a 2023, yaye mana ƙunci da baƙin ciki tare da garkuwa tare da yara da manya da ake yi, tsadar rayuwa da sauran su.”
Gidauniyar agaji da ta ke shugabanta, wato ‘Today’s Life Foundation’, ita ce ke jagorantar shirya gangamin.
Wannan sabon yunƙurin na Mansurah ya biyo bayan yadda ‘yan ta’adda su ka tare wata mota ƙirar bas wadda ke kan hanyar zuwa Kaduna daga Sakkwato a ranar Litinin da ta gabata a ƙauyen Gidan Bawa da ke cikin Yankin Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, su ka ƙone mutum 23 da ke cikin motar har lahira.
Bidiyon kisan ya yaɗu a soshiyal midiya, kuma ya girgiza jama’a matuƙa.

Zamfara, Sakkwato Katsina, Kaduna da Neja dai su na daga cikin jihohin Arewa da wannan bala’i ya fi faruwa, ga kuma ibtila’in Boko Haram a Borno da Yobe.
A wasu saƙonni kamar biyar da ta wallafa a Instagram a yau, waɗanda mujallar Fim ta tattaro, Mansurah, wadda fitacciyar jarumar finafinai ce a da, ta bayyana matuƙar damuwa kan abin da ke faruwa, musamman da ta ga yadda aka ƙone matafiyan nan da ran su.
A saƙonnin nata, ta ce wa ‘yan ta’addan: “Menene talaka ya yi muku? Laifin me aka yi muku? Don Allah ku yi haƙuri. Don Allah ku yafe mana. Allah ya huci zuciyar ku.
“Mutum ya ƙona mutum ɗan’uwan sa a raye? Ta yaya? Kuma ku na kallo su ka ƙone ƙurmus, ba imani ba tsoron Allah. Watau ba ku damu da haɗuwar ku da Ubangiji Allah ba. Ku tuba wallahi, zai yafe muku.
“Mutanen da ku ke kashewa, na abinci su ke nema. Ba su da hannu a abin da ya ke faruwa a ƙasa, su ma ana tauye musu haƙƙin su kamar ku.”
Daga nan, don kada “maganar ta ƙare a soshiyal midiya” ko tura saƙo kawai a shafukan sada zumunta, sai furodusar ta bayyana ƙudirin kiran taro domin kai kuka ga Ubangiji (s.w.t.) inda ta ce, “Inshaa Allah za mu haɗa malamai ranar Asabar a yi saukar Alƙur’ani sau 9 a Filin Sukuwa (na Kano) da misalin ƙarfe 10 na safe.”
Ta ce, “Mu na sa rai bayan saukar za mu yi yanka a wajen a bayar sadaka domin Allah ya karɓa mana.”
Haka kuma Mansurah ta ce sun fara tuntuɓar malaman da za su halarci taron a Kano, sannan su na ƙoƙarin tara kuɗin da za a sayi san da za a yanka.
Ta yi kira ga mahalarta duk wanda zai iya ya zo da abinci kamar waina, fanke, sinasir, ruwan sha da sauran su.
Ta bayyana cewa Kwamishinan ‘Yansanda ya amince da wasiƙar da ta kai masa ta neman izinin yin taron addu’ar a ranar Asabar.
A game da yadda sauran jama’ar jihohin Arewa waɗanda ba a Kano su ke ba za su iya shiga wannan gangamin, Mansurah ta yi kira ga masu sha’awar shiga a yi da su da su fito su bayyana kan su.
Ta yi nuni da cewa wannan taron addu’a ba su kaɗai a Kano za su yi shi ba.
Ta ce, “Ba mu kaɗai za mu iya ba. Yanzu ya dace mu yi, idan ba haka ba ba za mu taɓa iya yi ba.

“Mun dai ga abin da ya faru ga waɗannan mutane waɗanda ba su ji ba ba su gani ba. Ba za mu iya yin shiru ba. Mu ci gaba da addu’a. Mu fito mu yi wannan abu don Allah.”
A cikin alhini, Mansurah ta ce, “Kada ku ɗauka cewa ba mu isa mu yi wannan abu ba. Ku yi wannan abu saboda Allah.
“Ku yi wannan abu saboda mutanen da ba su ji ba ba su gani ba amma su ke mutuwa a kullum. Ku yi wannan abu saboda ƙananan yaran da ake kanawa ana garkuwa da su. Ku yi wannan abu saboda tsaron lafiyar ku. Ku yi wannan abu saboda ‘ya’yan ku don Allah. Ku yi wannan abu saboda ƙasar ku.”
A ƙarshe ta yi addu’a kamar haka: “Allah ya ba wa ƙasar mu zaman lafiya, Allah ya kawo ƙarshen wannan abu a arewacin Nijeriya,” kuma “Allah ya jiƙan waɗanda su ka mutu, ameen.”

Ya Allah kasawa mansurah isah da alkhairi.
Gaskiyya nagoyi bayanka mal nasir sarkin waka akan rufe tiktok. Allah yasaka da alkhairi.
Mal muhibbat inamiki fatan wasu shekarun masu albarka.amen