SABIRA Mukhtar ta na ɗaya daga cikin jarumai mata da ake ganin nan gaba kaɗan za su zamo manya a fagen harkar fim a Kannywood saboda irin ƙoƙarin da su ke nunawa a finafinai. Ita ce jarumar fitaccen fim ɗin nan ‘Fanan’ wanda Mansurah Isah ta ɗauki nauyin shiryawa a cikin 2021 inda ta fito tare da Sani Musa Danja. Duk da yake ba shi ne fim ɗin ta na farko ba, amma dai shi ne ya fito da ita har duniya ta san ta.
A wannan tattaunawar da ta yi da mujallar Fim, Sabira ta bayyana yadda aka yi ta shigo harkar fim da yadda ‘Fanan’ ya ɗaga darajar ta har ya zamo abin alfahari a gare ta, da kuma burin ta a harkar fim.
FIM: Da farko za mu so ki gabatar da kan ki ga masu karatun mu.
SABIRA MUKHTAR: To, ni dai suna na Sabira Mukhtar, kuma ni haifaffiyar garin Kano ce. A nan na tashi na yi karatun firamare da sakandare har zuwa jami’a.
FIM: Ya aka yi ki ka samu kan ki a cikin masana’antar Kannywood?
SABIRA MUKHTAR: To, gaskiya na samu shiga harkar fim ne ta dalilin furodusa Abdul Amart, wanda tun kafin na shigo mu na mutunci da shi, to kuma da zan shigo sai ya zame mini hanya.
FIM: Wannan ya nuna tun kafin ki fito a ‘Fanan’ kin yi wasu finafinai a baya.
SABIRA MUKHTAR: E, gaskiya na yi wasu finafinan, ba shi ba ne na farko. Duk da cewar a yanzu ba zan iya kawo su duka ba, amma dai zan iya tunawa na fito a fim ɗin ‘Ranar Rabuwa’, wanda shi na fara fitowa a matsayin jaruma. Amma na san duk cikin finafinan da na yi babu wanda ya fito da ni aka san ni sai fim ɗin ‘Fanan’, don haka ne ma wasu sai a fim ɗin su ka fara sani na duk da cewar na daɗe. Kuma akwai wasu finafinan da na fito a matsayin jaruma, amma dai ina ganin yanzu ne lokacin nawa ya zo.

FIM: Ya aka yi ki ka samu shiga fim ɗin ‘Fanan’?
SABIRA MUKHTAR: E, na samu kai na a cikin fim ɗin ‘Fanan’ ne ta dalilin furodusar fim ɗin, Mansurah Isah, wadda ita ce ta kira ni ta faɗa mini cewar ta na son na fito a rol ɗin Fanan a fim ɗin saboda na yi daidai da rol ɗin. Don haka ina godiya a gare ta. Babu abin da zan ce da ita sai dai Allah ya saka mata da alheri.
FIM: Rawar da ki ka taka a ‘Fanan’ ta sa fuskar ki ta fito kowa ya san ki. Ko ya ki ke ganin tasirin fim ɗin a rayuwar ki?
SABIRA MUKHTAR: To gaskiya na ji daɗi sosai fiye da yadda ka ke tunani, don ban taɓa tunanin zan samu ɗaukaka a cikin ɗan lokaci kaɗan ba, don haka ko lokacin da ake nuna shi a sinima idan na ga yadda mutane su ke son su gan ni ina jin daɗi sosai, har na ke ji a zuciya ta wai ni ce ake zuwa ana kallo na har ana yin hotuna da ni saboda na zama jaruma! Don haka har hawaye ne ya ke zuba daga ido na. Don haka gaskiya fim ɗin ya yi mini tasiri sosai. Ina alfahari da shi. Don fim ɗin ya ɗaukaka ni a daidai lokacin da ban zata ba.
FIM: Ko a wajen ɗaukar fim ɗin kin sha wahala sosai ganin cewar fim ɗin cike ya ke da abin tausayi?
SABIRA MUKHTAR: E to, gaskiya zan iya cewa na sha wahala, kuma a wani wajen ban sha wahala ba. Kuma ko da na sha wahala a wajen aikin, to sakamakon da na samu na nasara daga baya ya sa ba na ganin wahalar, don haka ma na manta da wahalar da na sha.
FIM: A cikin aikin me ya fi burge ki?
SABIRA MUKHTAR: Gaskiya abin da ya fi burge ni shi ne yadda na yi aiki da daraktan ba tare da ya nuna mini wani abu na takura ba. Har mu ka gama ina cikin jin daɗi, don ko da wani abu na yi ba daidai ba, to sai ya nuna mini cikin sauƙi yadda zan fahimta. Don haka mun yi aikin fim ɗin cikin sauƙi da kwanciyar hankali.
FIM: A farkon fim ɗin an nuno ki a matsayin matar da mijin ta ya ke azabtar da ita. Ko yaya ki ka kalli kan ki a wannan matsayin?
SABIRA MUKHTAR: To gaskiya ni kai na sai da na ji tausayin kai na, saboda ban taɓa yin rol irin wannan ba, don haka sai abin ya ba ni tausayi. Kuma na yi mamaki ma da har na iya gudanar da aikin.
FIM: A ƙarshen fim ɗin kin zamo matar babban mai kuɗi, ko?
SABIRA MUKHTAR: E, gaskiya ne. Hakan ya nuna cewar wahala ba ta ɗorewa, kuma daɗi ma haka, don irin saƙon da fim ɗin ‘Fanan’ ya ƙunsa kenan.

FIM: Yanzu da ya ke ‘Fanan’ ya fito da ke, ko wane irin buri kI ka sa a gaba?
SABIRA MUKHTAR: To, buri na dai na ƙara yin nasara a gaba, don haka kullum addu’a na ke yi Allah ya ƙara ɗaukaka ni, kuma ina fatan komai zai zo mini cikin sauƙi.
Kuma ina fatan masoya na za su taya ni da addu’a Allah ya ƙara ɗaukaka ni a cikin harkar fim ɗin.