MARYAM Tasi’u Sulaiman (Habeebti) matashiyar mawaƙiya ce wadda ke zaune a Mulumfashi, Jihar Katsina. Ta kai aƙalla shekara takwas a cikin harkar waƙa, sai dai kuma ba kowa ya san ta ba, kasancewar ta na zaune a garin su. Sai a wannan lokacin ne ta fara fitowa.
Habeebti dai kyakkyawa ce, son kowa ƙin wanda ya rasa. Hasali ma duk inda ta shiga kowa so ya ke ya yi mu’amala da ita saboda ta na da fara’a da sakin fuska ga kowa. Sai kuma Maryam ba ta bari a raina ta ko a ci mutuncin ta.
Mujallar Fim ta tattauna da mawaƙiyar kwanan nan a Kaduna, inda ta yi mana bayani kan yadda aka yi ta tsinci kan ta a harkar waƙa da burin ta a nan gaba. Ɗaya daga cikin abubuwan da ta faɗa mana shi ne yadda har ta fara shiga cikin fim a matsayin ‘yar wasa.
Ga yadda hirar ta kasance:
FIM: Ki faɗa wa masu karatu tarihin rayuwar ki a taƙaice.
MARYAM TASI’U: Ni suna na Maryam Tasi’u Sulaiman, amma ana kira na da Habeebti. An haife ni a Malumfashi, Jihar Katsina. Na yi firamare na a ‘Destiny Primary School’, Malumfashi, na yi ‘Junior Secondary School’ ɗi na a Kabomo, na yi ‘Senior section’ ɗi na a GG, sannan na zo na ida a ‘Kabomo Salvation International School’, Kinkinau.
FIM: Me ya sa ki ka shiga harkar waƙa?
MARYAM TASI’U: Da farko dai gaskiya ‘brother’ na ne ya fara kai ni wurin da na fara yin waƙa, daga baya na ga ya kamata ni ma in ɗan gwada da kai na tunda ban san baiwar da Allah ya ba ni a kan ta ba, wataƙila zan iya taimakon wani ta wata hanyar ko kuma ga ni karan kai na. Allah ya sa hanyar da na ɗauka ta na da albarka, ya kuma sa min albarka a cikin ta.

FIM: A wane situdiyo ki ka fara waƙa?
MARYAM TASI’U: Gaskiya na fara waƙa a situdiyon wani Abdullahi Hussaini Danko, a nan na yi waƙa tare da yaya na uwa ɗaya uba ɗaya, Aliyu. Waƙar da mu ka yi sunan ta ‘Dace Da Masoyi’. Ita ce waƙa ta ta farko. Daga baya na zo na ɗan daina waƙa na wani ɗan lokaci. Sai kuma na bar wannan situdiyon na koma situdiyon ‘Mudu Musical Studio’, wurin Kamal 3Star. A nan ne na yi waƙoƙi da yawa.
FIM: A wace shekara ki ka fara waƙa?
MARYAM TASI’U: Na fara waƙa ne a shekarar 2014.
FIM: Ban da waƙar da ki ka yi tare da yayan ki, wace waƙa ki ka yi ta karan kan ki?
MARYAM TASI’U: Da waƙar auren ƙanne na ne guda biyu, Hajara da kuma Safara’u. Sai kuma waƙoƙin siyasa da na yi guda biyu.
FIM: Ya ki ka ji a lokacin da aka umarce ki da ki shiga ɗakin da ake ɗaukar waƙa?
MARYAM TASI’U: Ai tun daga lokacin da ya ce mani mu je zan yi masa amshin waƙa, gaskiya abin ya ba ni tsoro saboda ban taɓa yi ba, shi ne ‘first time’ ɗi na. Da farko na kalli abin, ta yaya zan shiga, abin da ba ka saba ba ka san zai zame maka wani iri. Da farko da na fara, sai jiki na ya fara rawa, kawai na aje na fito. Daga baya kuma da ya kasance sai ni da yaya na ɗin da kuma mai ɗaukar muryar sai na saki jiki, ina ɗora ɗango ɗaya, biyu kawai na ga na wuce gaba ɗaya, sai na ga ba ma wani abu ba ne. Tun daga nan kuma sai na ci gaba da yi ba ɗarɗar a tare da ni.
FIM: Yawancin mawaƙa mata rubuta masu waƙa ake yi. Ke ki ke rubuta naki waƙoƙin ko kuma rubuta maki ake yi?
MARYAM TASI’U: Gaskiya wani lokacin na kan ba ƙane na ko kuma yayan nawa ya rubuta mani, wani kuma ni na ke rubutawa da kai na, inda na samu kuskure sai su gyara mani, saboda ai yanzu na ke tashi ban gama sanin yadda abin ya ke ba, su kuma sun daɗe a cikin abin.
FIM: Ko a cikin waƙoƙin da ki ka yi akwai wadda ta yi fice?
MARYAM TASI’U: Gaskiya sai dai waƙoƙin bikin da na yi, saboda na siyasan da na yi ban fitar da su ba, ta Gwamna Malam Nasiru El-Rufa’i da kuma Jafar Sani, Kwamishinan Muhallin Jihar Kaduna.
FIM: Waƙoƙin biki da siyasa kawai ki ke yi kenan?
MARYAM TASI’U: Duka ina yi. Ina yin na soyayya, siyasa, aure da sauran su. Ka san duk wanda ya zo gaban ka shi za ka yi, don ba ka san inda abincin ka ya ke ba. Kuma lalube ne a cikin duhu, sai dai fatan nasara.
FIM: Ki faɗa mana sunayen wasu daga cikin waƙoƙin ki.
MARYAM TASI’U: Kamar yadda na faɗa maka, akwai “Dace Da Masoyi”, “Mahaɗin Rayuwa”, “Gwamna Nasiru El-Rufa’i”, “Jafar Sani”, da sauran su dai.
FIM: Aƙalla waƙoƙin da ki ka yi za su kai nawa?
MARYAM TASI’U: Gaskiya za su kai talatin da wani abu.
FIM: Wane fitaccen mawaƙi ki ke da burin yin waƙa tare da shi?
MARYAM TASI’U: Wannan kuma ba ka ‘selecting’, sai dai duk wanda Allah ya haɗa ka da shi ka yi ƙoƙarin sanin yadda za ka zauna da shi. Zama lafiya da mutane shi ne ya fi komai, kuma shi ke sanyawa mutane su so ka, sannan su ja ka a jiki. Fatan mu kullum Allah ya haɗa mu da nagari, waɗanda za su ji tausayin mu kuma su jiƙan mu.
FIM: Kin taɓa yi wa wani fitaccen mawaƙi amshi?
MARYAM TASI’U: Gaskiya ban taɓa ba.
Ka yi taka-tsantsan da rayuwa, saboda lokaci ya koma ba a kiwon dabba, mutum ake kiwo. Don haka tun kafin a yi maka wa’azi ka yi wa kan ka, sannan kuma ka san da wa ka ke zaune, ka san wace irin mu’amala za ka yi da shi. Duk inda ka tsinci kan ka, ka yi ƙoƙari ka ba kowa girman sa, ka mutunta kowa don ba ka san wace irin hikima wani ya ke da ita da za ka ƙaru da shi ba. Allah ya haɗa mu da mazauna nagari
FIM: Idan wani mawaƙin na neman ki don ku yi aiki tare, ta wace hanya zai bi don ganin ya same ki?
MARYAM TASI’U: Gaskiya ban san ta yadda zan ce ba, domin ka san wani lokacin Hausa na ga dai shi nan ne, ba wai bai zauna mani ba ne, ka san Kaduna ba ku da Hausa! (dariya)
FIM: Sai ki yi Hausar da kowa zai fahimta. Abin nufi ki na da wani manaja ne ko kuma ubangida da za a nema idan ana so a yi aiki da ke?
MARYAM TASI’U: E to, ba zan ce ga shi ba, don ni yanzu neman ɗagawa na ke yi. Sai yaya na da mu ke tare, kuma shi ma yanzu ba a gari ɗaya mu ke ba. Ni ina Malumfashi, shi kuma ya na Bichi ta Jihar Kano, ka ga ba zan iya cewa a neme shi ba.
FIM: Daga lokacin da ki ka fara waƙa zuwa yanzu waɗanne irin nasarori ki ka samu?
MARYAM TASI’U: Alhamdu lillahi, nasara kam ana samu, domin duk wanda aka ce zai fara abu iyaye sun sa masa hannu ba ƙaramar nasara za ka riƙa samu a ciki ba. Kuma kai ma ka riƙa addu’a, sannan ka yi taka-tsantsan da rayuwa, saboda lokaci ya koma ba a kiwon dabba, mutum ake kiwo. Don haka tun kafin a yi maka wa’azi ka yi wa kan ka, sannan kuma ka san da wa ka ke zaune, ka san wace irin mu’amala za ka yi da shi. Duk inda ka tsinci kan ka, ka yi ƙoƙari ka ba kowa girman sa, ka mutunta kowa don ba ka san wace irin hikima wani ya ke da ita da za ka ƙaru da shi ba. Allah ya haɗa mu da mazauna nagari.
FIM: A ɓangaren ƙalubale fa?
MARYAM TASI’U: Gaskiya da farko da zan fara waƙa na ji tsoron fara wannan hidimar, saboda ina ganin kamar iyaye na in su ka sani za su ji haushi. Sai na ke yi a ɓoye. Daga baya mahaifi na ya kira ni, ya ce kwana biyu ba ya gani na a gida, me ya ke faruwa ne? Sai na ke faɗa masa gaskiya tsakani da Allah ba zan ɓoye masa ba, ga ni da ya ke yi ba na zama, gaskiya wuri kaza na ke zuwa a kan hidimar waƙa. Daga nan ya ce Allah sanya albarka, sannan ya ce duk abin da zan yi in yi taka-tsantsan. Ya yi mani nasiha. Ni dai zan yi abin da zan samu kuɗi na halak, zan yi shi matsawar bai saɓa wa addini ba, kuma zan kare wa kai na mutunci.
FIM: Wace fitacciyar mawaƙiya ce ki ka fi son waƙar ta ko kuma ki ka fi jin daɗin muryar ta a waƙa?
MARYAM TASI’U: Gaskiya ba ni da zaɓi.
FIM: Ganin cewa ga ki matashiya kuma kyakkyawa, ko ki na da burin fitowa a fim?
MARYAM TASI’U (dariya): Gaskiya ba ni da zaɓi a kai. Duk abin da Allah ya kawo mani, ina maraba da shi. Ni kamar lalube na ke yi a cikin duhu. Ban san wanne ne idan na ɗauka zai zame mani hanyar abinci na ba. Ina fatan dukkan abin da zai zama alkhairi a gare ni Allah ya tabbatar mani da shi. Idan babu alkhairi kuma Allah ya musanya mani da mafi alkhairi.

A yanzu ma na samu damar shiga wannan fitaccen fim ɗin na mawaƙi Lilin Baba, wato ‘Wuff’. Kuma alhamdu lillah, an samu abin da ake so. Ina kuma fatan Allah ya sa na fara fitowa a sa’a.
FIM: A ƙarshe, me za ki ce wa abokan sana’ar ki?
MARYAM TASI’U: Ina yi mana fatan alkhairi baki ɗayan mu. Allah ya sa mana albarka a kan abin da mu ka sa a gaba.