TSOHUWAR jaruma a Kannywood, Hajiya Zakiyya Ibrahim, ta bayyana cewa ta na samun alheri bakin gwargwado tun daga lokacin da ta koma cin tudu biyu, wato ta rikiɗe daga jarima ta koma mawaƙiya.
Ya zuwa yanzu dai ta yi waƙoƙin siyasa masu yawa, inda ta fi samun kuɗi, ban da na yabon Manzon Allah (s.a.w.) da na soyayya waɗanda su ma ta yi su da dama.
Haka kuma jarumar, wadda ta daɗe ana damawa da ita a Kannywood, furodusa ce wadda ta shirya finafinai masu yawa nata na kan ta.
A tattaunawar da mujallar Fim ta yi da ita, Zakiyya ta ce: “Kamar yadda na daɗe ina yin fim a matsayi na na jaruma, kuma haka na daɗe ina ɗaukar nauyin shirya fim. To ita ma waƙar haka na daɗe da ita.”
Ta ci gaba da cewa, “Tun a 2008 na fara waƙa lokacin da aka buɗe ‘Hikima’.

“Don ba zan manta ba, a lokacin ne Sani Lawan Ƙofar Mata ya sa Aminu Ala ya yi album na waƙoƙin Malam Shekarau. To, ina cikin waɗanda su ka yi amshin waƙar, kuma tun daga wannan lokacin sai na fara tunanin yadda zan fara shirya tawa ta kai na, don ka san a lokacin masana’antar ta shiga wani hali. Don haka sai na fara da waƙar yabon Manzon Allah, wadda na bayar aka rubuta mini. Kuma daga nan sai na shiga waƙoƙin fim har na riƙa sayarwa, wasu kuma ina yin amfani da su a cikin finafinan da na ɗauki nauyin su, kamar waƙoƙin da su ke cikin fim ɗin ”Yar Asali’ duk ni na yi su. To da haka dai na fara har na zama mawaƙiya.”
Dangane da waƙoƙin da ta fi yi a yanzu kuwa, Zakiyya ta ce, “A gaskiya tun daga shekarar 2019 na fi mayar da hankali na a kan waƙoƙin siyasa, saboda su ne za ka yi a biya ka, tunda yanzu babu kasuwar sidi, to a haka na yi wa ‘yan siyasa masu yawa waƙa da gwamnoni da ‘yan majalisa.
“Kuma gaskiya ina samun alheri sosai.
“Sannan kuma na buɗe shafi na na YouTube ina saka waƙoƙin da na ke yi. Don haka ina samun cigaba sosai.”
Zakiyya, wadda a Kano ta ke da zama, ta ja hankalin abokan sana’ar ta da su guji abin da zai riƙa jawo masu magana, sannan su kuma jama’a su daina kallon ‘yan fim a matsayin lalatattu, domin duk wanda ka ga ya na yin wani abu da bai dace ba, to da man can tun a gidan su lalatacce ne.
“Mu ‘yan fim mu na da tarbiyya,” inji ta.
Comments 4