• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC da Hukumar Sadarwa za su magance matsalar da ka iya tasowa yayin aika sakamakon zaɓen 2023 ta hanyar BVAS

by DAGA WAKILIN MU
December 4, 2022
in Nijeriya
0
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (a tsakiya), da sauran jami'an hukumar a taron ganawa da manema labarai

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (a tsakiya), da sauran jami'an hukumar a taron ganawa da manema labarai

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta sha alwashin cewa yanzu haka ta na aiki tare da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) domin magance duk wani cikas da za a iya samu yayin aikawa da sakamakon zaɓen 2023 ta hanyar tsarin yaɗa sakamakon ƙuri’u ta na’urar BVAS.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, shi ne ya bayyana haka, ya na mai cewa an fara shiri tun a yanzu domin magance ko da wata matsala za ta bijiro saboda matsalar wuraren da saƙonni ta fasahar zamani ke wahalar isa, wato matsalar ‘network’.

Yakubu ya bayyana haka ne a Legas lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.

Wannan ƙarin haske da shugaban na INEC ya yi, ya biyo bayan damuwar da wasu ‘yan Nijeriya su ka fara nunawa cewa za a iya samun matsala da tsarin BVAS a yankunan da ke fama da cikas ɗin samun saƙo ko yaɗa saƙon ta fasahar zamani.

Yakubu ya ce a ranar Talata INEC za ta gana da jami’an hukumar sadarwa (NCC) dangane da yadda za a magance matsalar da ka iya tasowa wajen aika sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da BVAS.

Ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa kada su yi fargabar komai dangane da nagartar da zaɓen 2023 zai yi, ta hanyar amfani da BVAS.

Taron INEC da manema labarai a Legas

Ya ce: “INEC ta gano waɗansu wuraren da ke da matsalar ingancin ‘network’ da kuma wuraren da babu ‘network’ ɗin kwata-kwata. Kuma mu na nan mu na aikin tabbatar da cewa ba a samu wata matsala wajen aika sakamakon zaɓen yankunan ba.

“Mu na ta aiki da jajircewar ganin tabbas mun aika dukkan saƙonnin sakamakon zaɓe ko ina a faɗin ƙasar nan.”

Tun da farko sai da Kakakin Yaɗa Labarai na INEC, Mista Festus Okoye, ya roƙi kakafen yaɗa labarai su taimaka wa hukumar zaɓen ta hanyar daƙile bayanan ƙarya da labaran shaci-faɗin da ake dangantawa da INEC.

Ya ce ga shi dai bai fi sauran kwanaki 85 a yi zaɓe ba, amma labaran bogin da ake yaɗawa kan INEC abin damuwa ne sosai.

Loading

Tags: BVASFestus OkoyeINECmahmood yakubumatsalar netuwokNCCnetworksadarwa
Previous Post

Zaɓen ƙungiyar furodusoshin Arewa ta Kano: Kowa ya ci ba hamayya

Next Post

Baƙin ƙabilu ne ke ɓata mana Kannywood, su na siyasantar da ita – Rashida Maisa’a

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Hajiya Rashida Adamu Abdullahi (Maisa'a)

Baƙin ƙabilu ne ke ɓata mana Kannywood, su na siyasantar da ita - Rashida Maisa'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!