SHUGABAN Ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), reshen Jihar Filato, Rabaran Fada Polycarp Lubo, ya yaba wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), inda ya ce a yanzu hukumar ta inganta, kuma ta kamo hanyar zama sahihiya abin dogaro wajen gudanar da zaɓe karɓaɓɓe.
Da ya ke jawabi wurin wani taron mabiya ɗariƙar Katoliƙa na Pankshin da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Kanke, Lubo ya ce yanzu dai INEC ta inganta, kuma maguɗi ya ragu sosai a wurin zaɓe.
Da ya ke jawabi wurin taron mai taken “Hanyoyin Dacen Samun Gwamnati Tagari, Zaman Lafiya da Ci Gaban Ƙasa”, ya yi kira ga Kiristoci cewa kowa ya tashi ya mallaki katin rajistar zaɓe, domin a zaɓi mutane nagari a kan mulki.
Ya zaburar da Kiristoci su tashi su mallaki katin zaɓe, don huce takaicin su wajen zaɓen shugabanni nagari.
Shugaban ƙungiyar ya jaddada wa Kiristoci cewa hanya ɗaya da a yanzu za su samu shugabanni nagari, ita ce su tashi su mallaki katin zaɓe, domin zaɓen nagari a kan muƙamai daban-daban.
Rabaran Lubo ya ce, “Mallakar katin zaɓe ne kaɗai hanyar da Kiristoci za su bi domin su zaɓi shugabannin ƙwarai kuma nagari.
“Yanzu Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta ƙara gyaruwa, ta kuma ƙara inganci. Irin yawan maguɗin zaɓen da aka riƙa yi a baya, yanzu duk ya ragu sosai.
“Sannan kuma samuwar wannan sabuwar Dokar Zaɓe da aka sa wa hannu zai ƙara canja abubuwa da dama.
“Saboda haka ƙuri’un ku su ne makaman ku, kuma su ne ƙarfin ku na samun shugabanni nagari.
“A da ne ake cewa ƙuri’a ba ta da wani tasiri. Amma a yanzu dai ƙuri’a ce ke da tasiri, ba maguɗi ba.”
Rabaran Lubo ya kuma yi wa Kiristocin da ke kan muƙamai daban-daban na mulki cewa su ji tsoron Ubangiji, su yi gaskiya da kuma riƙe amanar da aka ba su.