• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta bayyana matsayin ta kan gyaran iyakokin mazaɓu

by DAGA WAKILIN MU
March 6, 2021
in Nijeriya
0
INEC za ta yi wa ma’aikatan faɗakarwa bita kan faɗakarwa
0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa Mai Cin Gashin Kan ta (INEC) ta bayyana irin aikin da ya rataya a wuyan ta wajen aikin gyaran iyakokin mazaɓun da ke ƙasar nan.


Babban Kwamishinan Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da kan Jama’a na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.


Okoye ya ce hukumar ta lura da wasu rahotanni da ke yawo a kafafen yaɗa labarai daban-daban a kan haƙƙoƙin hukumar wajen rarrabawa, sake nazari da kuma gyara kan iyakokin mazaɓu a Nijeriya.


Ya ce ganin haka ne ya sa tilas hukumar ta ga ya kamata ta fito ta bayyana matsayin ta a bisa tsarin mulki a wannan aikin.


Ya ce, “Saboda a tabbatar da fahimtar jama’a kan al’amarin, hukumar na so ta yi bayanin abin da tsarin mulki ya ɗora mata da kuma abin da ta ke yi a kan hakan.


“Da yake karkasa ƙasar nan zuwa zuwa mazaɓun Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da Majalisun Jihohi haƙƙin hukumar ne, da zaran an fitar da su, sauran aikin sake nazarin mazaɓun tare da ko yi masu kwaskwarima aikin haɗaka ne na ita hukumar da Majalisar Tarayya.

“Saboda haka, duk wani sake tsari ko gyara irin wannan ba zai yiwu ba sai ɓangarorin nan biyu na Majalisar Tarayya sun amince da shi, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.”


Okoye ya bayyana cewa a dalilin wannan muhawarar, hukumar ta na zantawa da  kwamitocin Majalisar Tarayya da su ka dace  domin a shirya zama da shugabannin majalisar saboda a tunkari wasu daga cikin manyan matsalolin rarrabawa da sake nazari da kuma gyaran mazaɓun a Nijeriya.


A cewar sa, wasu daga cikin matsalolin, waɗanda a baya hukumar ta nuna wa Majalisar Tarayya su, sun haɗa da waɗannan: “Tsarin Mulki na 1999 (a yadda aka yi masa kwaskwarima) bai ɗora wa INEC alhakin sake nazari ko sauya kan iyakokin mazaɓu ba bayan kowane shekara 10, kamar yadda aka faɗa a wasu ra’ayoyi a kafafen yaɗa labarai. Don cire duk wani shakku, Sashe na 73 (1) na Tsarin Mulki ya tanadi cewa aikin zai riƙa faruwa jefi-jefi ‘mafi ƙarancin shekara 10’.”


“Hakan ya nuna cewa za a iya yin hakan ne kaɗai daga shekara 10 zuwa sama. Don haka, hukumar ba ta saɓa wa Tsarin Mulki ba, tunda dai za a iya sake nazarin ne a cikin shekara 10 kaɗai zuwa sama.


“Haka kuma Tsarin Mulki ya tanadi cewar hukumar za ta iya fara aikin sake nazarin da yin gyaran idan an gudanar da aikin ƙidayar jama’a ta ƙasa, ƙirƙiro jihohi ko idan Majalisar Tarayya ta zartar da Doka [Sashe na 73 (2)]. A yanzu babu ko ɗaya daga cikin waɗannan abubuwan da su ka faru.


“Aikin ƙidayar jama’a na ƙarshe da aka yi an yi shi ne a cikin 2006, kimanin shekara goma sha biyar kenan. 

“Hukumar ta na ganin cewa sake nazari ko tare da sake tsarin mazaɓun bisa  bayanan shekara 15 da aka tattara bai dace ba saboda kowa ya san saurin ƙarin yawan jama’a da ake samu a Nijeriya zai sa a ga shirme a duk wani sakamako da aka samu.


“Ko ma dai yaya ne, Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa ta na nan ta na ƙoƙarin sake wani aikin ƙidayar kuma akwai alamar dacewar a jira a ga sakamakon shi.


“Ta wani ɓangaren, ba a ƙirƙiro wasu sababbin jihohi ba a Nijeriya tun daga lokacin da aka yi Tsarin Mulki a cikin 1999 sannan babu wata Dokar Majalisar Tarayya da aka yi mai buƙatar ɗ INEC ta fara aiki da wasu sassan Tsarin Mulki da su ka dace da batun karkasawa, sake nazari ko sake tsarin mazaɓun zaɓe.”


Kwamishinan hukumar zaɓen ya ƙara da cewa a kan batun mazaɓun jihohi da za a ƙirƙira a kowace jiha ta tarayyar ƙasar nan, Tsarin Mulki ya tanadi cewa yawan waɗanda za a yi a kowace jiha ya kasance ninki sau uku ko sau huɗun yawan mazaɓun tarayya (kujerun Majalisar Wakilai), ya danganta da mafi ƙarancin 24 da kuma mafi yawan 40.


A cewar sa, matsalar ita ce wasu jihohin a yanzu su na da yawan kujerun su har sau uku a Majalisar Wakilai, wasu sau huɗu; wasu kuma su na da mafi ƙarancin  24 yayin da wasu har sun kai ƙurewar 40.


“Wasu, yawan mazaɓun su na Majalisar Jiha bai kai sau uku ko huɗu na yawan kujerun su na Majalisar Wakilai ba.

“Wannan kwamacalar gudunmawar na buƙatar a yi cikakken ƙarin bayani kan karkasawa, sake nazari da yin kwaskwarima ga iyakokin mazaɓun, wanda a gaskiya ya na buƙatar gyaran tsarin mulki.”


Okoye ya yi nuni da cewa akwai kuma batun mazaɓun da ake cewa an danne waɗanda mazaɓu ne da ake da su a da tun kafin a samar da Tsarin Mulki na 1999.


A cewar sa, mutanen da ke kamfen ɗin a ƙirƙiro masu da waɗannan mazaɓun su na cewa an “danne” su ne a halin da ake ciki ba.


Ya ce, “An shigar da ƙararraki arba’in da biyu a kotuna daban-daban a sassan ƙasar nan inda ake buƙatar a tilasta INEC ta ‘dawo’ da mazaɓu sittin da biyu.


“Hukumar ta na ta bayyana cewa batun ‘dawo da mazaɓu’ akwai ayar tambaya a kan sa a shari’ance sannan kuma akwai ayar tambaya wajen yiwuwar sa a zahirance.


“Akwai ayar tambaya a ce wai INEC ta dawo da mazaɓu waɗanda aka yi a ƙarƙashin wani tsohon tsarin mulki zuwa cikin na yanzu. Misali, Tsarin Mulkin yanzu ya tanadi cewa kujerun Majalisar Wakilai kada su haura wani yawa kuma ninki su ne a mazaɓun Malisar Jiha. Dawo da dukkan tsofaffin mazaɓu daga tsoffin tsarin mulki ba shakka zai nuna cewar yawan kujerun da Tsarin Mulkin yanzu ya tanadar zai ƙaru. 

“Bayan haka ma, akwai tsare-tsaren mulki daban-daban da aka yi a baya, kowanne da nasa iyakancewar yawan mazaɓun.


“Bugu da ƙari, wanne ne daga cikin tanadin abin da tsarin mulki za mu dawo da shi? Wataƙila wasu mutanen za su ma nemi a dawo da mazaɓu huɗun da ke Kalaba da Legas waɗanda aka ƙirƙira a cikin 1922 bayan an ƙirƙiro Tsarin Mulkin Clifford Constitution.


“Haka kuma ba daidai ba ne a yi maganar mazaɓun da aka danne saboda wasu daga cikin mazaɓun an raba ƙasar su a dalilin ƙirƙiro jihohi tare da gyaran kan iyaka, da ƙirƙiro Yankunan Ƙananan Hukumomi, da kuma ƙirƙiro  mazaɓun zaɓe da ake da su yanzu.


“Wasu daga cikin hukunce-hukunce da kotuna su ka yanke kan batun nan na mazaɓun da aka danne  sun amince da matsayar hukumar, yayin da wasu sun koma ga masu kamfen ɗin ‘mazaɓun da aka danne’. Sannan a wasu shari’un, hukumar ta ɗaukaka ƙara.


“Waɗannan su na daga cikin matsalolin da su ka takura hukumar a kan batun sake nazari da gyaran kan iyakokin mazaɓu. Duk da haka, ba wai hukuma ba ta sane da muhimmancin daidaita fitar da iyakokin mazaɓu ba a tsarin mulkin dimokiraɗiyya da tsarin gudanar da zaɓe ba.

“Amma dai waɗannan wasu al’amura ne masu sarƙaƙiya a shari’ance da siyasance da kuma zahirance. Hakan ne ya sa hukumar ta buƙaci ta zauna tare da shugabannin Majalisar Tarayya domin a warware waɗannan al’amuran, tare da samar da matsayar da ake buƙata wadda za ta tabbatar da cewa duk wani sake nazari da za a yi na mazaɓu zai samu amincewar Majalisar Tarayya, ba kamar yadda ake yi a baya ba inda majalisar ba ta amince ta buƙatun hukumar ba kan sake nazari da yin sauyi a mazaɓun.


Okoye ya bayyana cewa hukumar a yanzu haka ta na nan ta na tsara cikakken kundin tattaunawa kan waɗannan al’amura wanda zai taimaka wajen taron da za ta yi da Majalisar Tarayya.


Ya ce, “Hukumar ta na so ta bayyana wa duniya duk wata tattaunawa ta fahimtar juna da shugabannin kwamitoci daban-daban na Majalisar Tarayya da neman goyon bayan jama’a don tabbatar da an samu kyakkyawan yanayi da zai ba hukumar damar ci gaba da yin aikin ta a kan hakan.


“Don nanatawa, haka kuma hukumar na so ta bayyana cewa batun mazaɓun wani abu ne daban kuma bai da alaƙa da aikin tuntuɓar da ake yi yanzu kan samar da ƙarin yawan rumfunan zaɓe a Nijeriya.”

Previous Post

An sallami Ashiru Nagoma daga asibiti

Next Post

Yarjejeniya: Afakallah zai daina kama ‘yan fim haka barkatai

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Yarjejeniya: Afakallah zai daina kama ‘yan fim haka barkatai

Yarjejeniya: Afakallah zai daina kama 'yan fim haka barkatai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!