HUKUMAR Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta fara aikin horas da jami’an ta da ke shugabantar harkar zaɓe a jihohi 36 da Gundumar Birnin Tarayya a kan hanyoyin yawaita rumfunan zaɓe.
Babban Kwamishina a hukumar, Farfesa Okechukwu Ibeanu, shi ne ya bayyana haka a ranar Juma’a a wajen taron bitar kwana biyu da aka shirya wa jami’an a Abuja.
Ya ce an shirya taron bitar ne domin a ƙara wa jami’an ilimi kan ƙoƙarin da ake yi na mayar da ƙananan wuraren kaɗa ƙuri’a (voting points) zuwa rumfunan zaɓe a dukkan faɗin ƙasar nan.
Ibeanu, wanda shi ne shugaban Kwamitin Ayyukan Gudanar da Zaɓe a hukumar, ya ce taron bitar ya na da muhimmanci wajen aiwatar da hanyoyin da za a bi a faɗaɗa rawar da masu jefa ƙuri’a za su taka a harkokin zaɓe a nan gaba.
Ya ƙara da cewa horaswar wani muhimmin aiki ne wajen cimma manufar wata tafiya wadda aka fara ta watanni kaɗan da su ka gabata.
Ya bayyana cewa akwai buƙatu a rubuce har 10,092 da aka kai wa hukumar na samar da rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar nan.
Ya ce, “Damar samar da rumfunan zaɓe ga masu zaɓe ya na ta raguwa kuma ƙoƙarin da ake yi na yawaita su bai samu nasara ba saboda hukumar ba ta yi aiki da dabarar da ta dace ba a kan hakan.
“Don haka ake yin sabon ƙoƙarin fara tuntuɓa tare da aiki da masu ruwa da tsaki a faɗin ƙasar nan domin su amince a warware matsalar wadda ta shafi tsarin zaɓen a shekaru 25 da su ka gabata.”
Ibeanu ya ce a wajen yin hakan an fito da shawara to amma akwai buƙatar a aiwatar da shawarar domin a cimma muradi.
“Don a tabbatar da an bi shawarar a yadda ta ke, tilas ne a samar da isasshen horo ga jami’an da ke gudanar da zaɓe waɗanda su ne shugabannin harkar zaɓe a dukkan jihohin, waɗanda su ne za su aiwatarwar da shirin.
“Burin taron bitar shi ne ya tabbatar da cewa an ilmantar da su kan hanyoyin da ake so a bi wajen gudanar da aikin.”
Ibeanu ya ƙara da cewa ana sa ran shugabannin aikin za su maimaita horaswar a jihohin su ga jami’an da ke yankunan ƙananan hukumomi.
Ya ce ana so a kammala aikin horaswar kafin a fara aikin yi wa masu zaɓe rajista a ranar 28 ga Yuni.
Ibeanu ya ce INEC ta na aiki domin ta magance matsalolin da ke kawo cikas ga shigar masu zaɓe cikin tsarin zaɓe kafin a yi manyan zaɓuɓɓuka na ƙasa.
Shi ma a nasa jawabin, Babban Kwamishina na INEC kuma Shugaban Kwamitin Wayar Da Kan Masu Zaɓe da Yaɗa Labarai, Mista Festus Okoye, ya ce samar da rumfunan zaɓe zai samar da damarmaki masu yawa ga sababbin masu yin rajista ta yadda za su samu rumfunan zaɓe cikin sauƙi.
Okoye ya tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa INEC za ta ci gaba da tuntuɓar Majalisar Tarayya domin a gaggauta aikin yi wa Dokar Zaɓe garambawul.
A cewar sa, wannan zai sa a shigar da sababbin tsare-tsare da za su inganta shigar da masu zaɓe cikin tsarin a ƙasar nan.