• Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
Sunday, June 15, 2025
  • Login
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai da Rahotanni
    • Labarai
    • Rahotonni
    • Tattaunawa
  • Sharhi da Tsokaci
    • Sharhin Fim
    • Tsokaci
  • Masu Haskawa
    • Taurarin Fim
    • Marubuta
    • Mawaƙa
  • Addini da Rayuwa
    • Rayuwa
    • Iyalai
    • Al’adu
    • Addini
  • Ranar Murna
No Result
View All Result
Kannywood - News, reviews and more  › hausa
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

INEC ta sha alwashin zaɓuɓɓukan 2023 za su fi na baya inganci

by DAGA ALI KANO
July 20, 2022
in Nijeriya
0
Farfesa Mahmood Yakubu (na 5 daga dama) tare da maziyartan

Farfesa Mahmood Yakubu (na 5 daga dama) tare da maziyartan

0
SHARES
0
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsappShare on Telegram

HUKUMAR Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bada tabbacin cewa manyan zaɓuɓɓukan da za a yi a Nijeriya a baɗi sai sun fi duk waɗanda aka yi a baya nagarta.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya faɗi haka a ranar Talata a Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin jami’an wasu hukumomin tsara harkar zaɓe da su ka zo daga Amurka, wato ‘International Republican Institute’ (IRI) da’National Democratic Institute’ (NDI).

Ya ce zaman da su ka yi da maziyartan shi ne na karo na farko da INEC ta karɓi baƙuncin wasu masu ruwa da tsaki a harkar zaɓe tun bayan zaɓen gwamnan Jihar Osun da aka yi a ran Asabar, kuma ya yi alƙawarin hukumar za ta ɗora a kan nasarorin da ta samu a zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Farfesa Yakubu ya faɗa wa maziyartan nasa cewa: “Kyawawan kalaman ku sun ƙara mana ƙwarin gwiwa, amma har yanzu akwai babban aiki a gaban mu.

“Mu na ba ku tabbacin cewa za mu ci gaba da aiki tuƙuru fiye ma da na da domin gudanar da manyan zaɓuɓɓukan 2023.

Farfesa Mahmood Yakubu (a hagu) lokacin da ya karɓi baƙuncin Amurkawan a hedikwatar INEC

“Na saurari wasu daga cikin batutuwan da aka gabatar a nan, amma ƙila idan mun shiga zaman aikin da za mu yi akwai damar da za mu samu mu yi tsokaci kan wasu daga cikin batutuwan.’’ 

Yakubu ya kuma yi magana kan zaɓuɓɓukan gwamna da aka yi a Ekiti a watan Yuni da na Osun da aka yi a ranar Asabar.

Ya ce: “Dangane da shirin manyan zaɓuɓɓukan 2023, ina so in tabbatar maku da cewa sai da mu ka yi wa ‘yan Nijeriya alƙawarin cewa zaɓen Ekiti zai yi kyau, kuma sai ga shi zaɓen na Ekiti ya yi kyau. Mun yi alƙawarin zaɓen Osun zai ma fi kyau, sai ga shi zaɓen na Osun ya yi kyau fiye da wanda ya gabace shi. 

“Yanzu mu na maku alƙawarin cewa manyan zaɓuɓɓukan 2023 za su fi duk wani zaɓe da mu ka yi a baya inganci kuma mun sadaukar da kan mu wajen gudanar da zaɓe mafi nagarta.”

Tun da farko, sai da jagoran maziyartan, Mista Frank LaRose, wanda shi ne Sakataren Jihar Ohio ta ƙasar Amurka, ya yaba wa INEC kan ƙoƙarin da ta ke yi na inganta al’amarin zaɓe a Nijeriya.

LaRose, wanda kuma kwamishinan zaɓe ne a Jihar ta Ohio, ya bayyana wannan ziyara da ya fara kawowa a Nijeriya a matsayin wata babbar dama da ya samu ta koyon abubuwa. Ya yi kira ga INEC da ta ci gaba da inganta tsarin zaɓe na Nijeriya.

Ya ce: “Ina jagorantar maziyarta waɗanda manyan masana ne a harkar zaɓe daga yankin mu, da ma faɗin Amurka.

“Waɗannan maziyartan su na da tunani irin naku na cewa mutanen Nijeriya sun cancanci su ci gaba da samun zaɓe mai inganci babu murɗiya, karɓaɓɓe ga kowa, saboda haka mu na aiki domin shirya wa zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023.

“Mun samu damar kai ziyara a Osun saboda wannan shi ne karo na biyu da aka gudanar da zaɓe a ƙarƙashin sabuwar Dokar Zaɓe.

“Mun haɗu da Kwamishinan Zaɓe Mazaunin can (REC) a Osun kuma mun yi nazarin wuraren kaɗa ƙuri’a daban-daban a Ranar Zaɓe.

Wasu daga cikin maziyartan (Hotuna daga: INEC)

“Da farko dai, ina so in yaba wa dukkan ku saboda aikin da ku ke ci gaba da gudanarwa wanda za ku ci gaba da inganta shi. Mun san cewa a ko yaushe akwai buƙatar a inganta aiki.

“Sai dai kuma, akwai buƙatar mu fara da yin la’akari da ingancin da INEC ta ke ta ƙara samu don gudanar da zaɓe mai kyau; kuma wannan wani abu ne da mu ka gani da idanuwan mu, ba wai mun jira wani ya zo ya ba mu labari ba ne.”

Loading

Tags: Dokar ZaɓeElectoral ActFrank LaRoseHukumar ZaɓeINECInternational Republican Institutemahmood yakubumaziyartaNational Democratic InstituteOhioZaɓen 2023
Previous Post

Rikiɗar Ibrahim Musa Ɗanƙwairo daga waƙa zuwa attajirin mawaƙin da ba a taɓa yin kamar sa ba a ƙasar Hausa

Next Post

Lokacin da na fara fim an so a haɗa ni da iyaye na, cewar jaruma Shafa’atu Muhammad

Related Posts

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista
Nijeriya

Nijeriya tana kan hanyar farfaɗowar tattalin arziki da dawo da martabar ƙasa — Minista

June 13, 2025
Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa yekuwar rigakafin cutar ƙyandar Jamus

June 4, 2025
Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150
Nijeriya

Tinubu ya tura wakilai zuwa Neja kan ambaliyar Mokwa da ta halaka sama da mutum 150

May 31, 2025
Gwamnatin Nijeriya ta goyi bayan amfani da Ƙirƙirarrar Basira cikin ɗa’a a aikin jarida – Idris
Nijeriya

Gwamnatin Tarayya ta yi ta’aziyyar mutanen da suka rasu a ambaliyar garin Mokwa

May 30, 2025
Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris
Nijeriya

Babu wasu masu juya Tinubu ta bayan fage – Idris

May 25, 2025
Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris
Nijeriya

Shirye-shiryen Shugaba Tinubu Suna Buɗe Hanyar Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya – Idris

May 20, 2025
Next Post
Shafa'atu Muhammad, jarumar Kannywood

Lokacin da na fara fim an so a haɗa ni da iyaye na, cewar jaruma Shafa'atu Muhammad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

  • Home
  • Game Da Mu
  • Privacy Policy
  • Contact Us

© 2024 Mujallar Fim

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labari
  • Addini
  • Al’adu
  • Iyali
  • Marubuta
  • Mawaƙa
  • Nijeriya
  • Ranar Murna
  • Rayuwa
  • Sharhin Fim
  • Tattaunawa
  • Taurari
  • Tsokaci

© 2024 Mujallar Fim

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!