Nan da lokacin da za a gudanar a Nijeriya, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta samar da ƙarin rumfunan zaɓe a faɗin ƙasar.
Shugaban kwamitin wayar da kan masu zaɓe a hukumar (INEC), Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a Abuja.
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a cikin Agustan 2014 INEC ta gabatar da buƙatar samar da ƙarin rumfunan zaɓe guda 30,027, inda arewacin ƙasar za ta samu rumfunan zaɓe 21,615 yayin da kudu za ta samu 8,412.
Wannan ya janyo ce-ce-ku-cen da ya sa INEC ta watsar da shirin.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa a halin yanzu Nijeriya ba ta da isassun rumfunan zaɓe.