A SAFIYAR yau aka yi jana’izar mahaifin shahararren mawaƙin Kannywood, Ali Isah Jita, wanda ya rasu a daren jiya.
Alhaji Isa Jibril Kibiya ya rasu wajen misalin ƙarfe 11:30 na daren Juma’a, 5 ga Fabrairu, 2021 a gidan sa da ke unguwar Shagari Quarters cikin birnin Kano.
Ya rasu ya na da shekaru kimanin 75 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya.
Marigayin ya bar ‘ya’ya 33. Daga cikin su akwai Ali Jita da Abdullahi Isah Laja, wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya Da Fasaha ta Jihar Kano, wato Kano State Polytechnic.
An yi masa sallah wajen ƙarfe 9:00 na safe, daga nan aka kai shi maƙwancin sa a maƙabartar da ke Maidile.
Abokan sana’ar Ali Jita da dama sun halarci jana’izar, irin su Ali Nuhu, Abdul’aziz Ɗansmall, Aminu Alan Waƙa, Abdul Amart Maikwashewa da sauran su.
Ɗaya daga cikin ‘ya’yan marigayin, Abdullahi Isah Laja, ya shaida wa mujallar Fim cewa mahaifin su haifaffen Ƙaramar Hukumar Kibiya da ke Jihar Kano ne. Ya zo Kano ne dalilin karatun allo, daga bisani ya shiga sana’ar fawa, wato sayar da nama.
‘Yan fim da sauran jama’a sun fara samu labarin rasuwar Alhaji Isah ne daga sanarwar da Ali Jita ya bayar a Instagram a safiyar yau.
A sanarwar, wadda ya rubuta da Turanci amma mujallar Fim ta fassara, mawaƙin ya ce: “Inna lillahi wa inna ilahir raji’un! Ina baƙin cikin sanar da rasuwar mahaifi na Isah Jibril Kibiya, za kuma a yi jana’izar sa da misalin ƙarfe 9:00 na safe a gidan sa da ke lamba 8, unguwar Shagari Quarters, Kano. Allah ya yafe masa zunuban sa ya kuma ba shi mafificin wuri a cikin Aljannah.”
Nan da nan ‘yan fim su ka dinga tura hoton marigayin tare da na Ali Jita, su na miƙa ta’aziyyar su.
Allah ya yi masa rahama, su kama iyalin sa Allah ya ba su haƙurin jure wannan babban rashi, amin.
